An rufe dakunan siyar da magani 287 a jihar Kogi

0

Wani babban darekta a hukumar yi wa magunguna rajista na kasa ‘PRCN’ Stephen Esumobi ya ce sun rufe kanana da manyan dakunan siyar da magani 287 a jihar Kogi.

Ya ce hukumar sa ta yi haka ne ganin cewa masu harkar siyar da maganin basu da lasisi sannan babu wajen ajiya na kirki kuma ya ce jami’an su zasu kwaso wadannan magunguna domin adana su.

Stephen Esumobi ya ce za su bude wanda suka rufe amma fa sai sun bi ta hanyar da ya kamata, sannan ya yi kira ga duk wadanda ke da niyar bude sababin dakunan siyar da magani da ya tabbata ya cika sharuddan da hukumar ta gindaya.

Share.

game da Author