Ummah Shehu ta fadi gaskiya cewa da tayi ‘Yan wasan yanzu sun fi na da gogewa – Mansurah Isah

0

Tsohuwar Jaruma, kuma fitacciyar ‘yar Kannywood Mansurah Isah ta ce ba shakka Umma Shehu ta fadi gaskiya ne a martanin da ta maida wa Ummi ZeeZee cewa wai masu yin fina-finan Hausa yanzu sun fi na da gogewa.

Mansurah ta fadi haka ne da take zantawa da wakilin PREMIUM TIMES a Abuja in da tace ita bata ga wani abin musu a kai ba.

“ Idan ka duba yanzu jarumai na wannan zamani na ci gaba, sannan kuma ga ci gaban kimiyya da fasaha da kuma kimiyyar yanar gizo. Ba zaka hada da zamanin mu ba inda zaka wani fim din ma a wajen daukar sa ne ake gaya wa jarumi abin da zai yi ko fadi. Yanzo ko za a baka shi a rubuce kayi ta nazari har zuwa lokacin da za a fara daukar fim din. Sannan akwai kwarewa yanzu ba kamar da ba. Saboda haka ba zaka ha daba.”

“ Wasu daga cikin wadanda muka yi zamani da su har yanzu suna damawa a fagen fim din amma dai ai kai kanka ka san ba za su iya hada kansu da masu tasowa ba sai dai su buga abinda za su iya. Musamman mu mata da muke da kaiyadadden lokacin shanawa a rayuwa gaba dayan ta.”

Ta yabawa jaruman wannan lokaci da yin kira garesu da su mai da hankali a sana’ar domin ganin kannywood ya ci gaba.

Share.

game da Author