Mutane 16 sun rasa rayukan su a hare-haren Maiduguri

0

Rundunar ‘Yan sandan Jihar Barno ta tabbatar da harin bam da aka kai Muna Garage da yayi sanadiyyar mutuwar mutane 13 da wasu wasu biya da suka sami rauni.

Bayan haka kuma kwamishinan ‘yan sanada na jihar Damian Chukwu ya ce wasu mata sun tada bam dake daure a jikin su.

Ya ce mutane 16 suka rasa rayukan su a hare-haren sannan wasu 18 sun sami raunuka dabam-dabam kuma suna samun kula asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri.

Share.

game da Author