Sai fa mun yi zanga-zangar mu a Sokoto domin doka ya bamu ikon yi- Shi’a

0

Mai magana da yawun kungiyar ‘Yan uwa musulmai Ibrahim Musa ya yi tir da yadda gwamnatin jihar Sokoto ta hana su gudanar da zanga-zanga Kamar yadda suka saba yi.

Ya fadi hakan ne ranar Alhamis inda ya kara da cewa kungiyar ‘ ba ta shirin gudanar da zanga-zangar da zai taba zaune tsaye a jihar.

Ibrahim Musa ya ce gwamantin jihar Sokoto ta bi sahun sauran jihohin arewa don hana su gudanar da zanga-zanga.

Atone-Janar kuma kwamishinan shari’a na jihar Sulaiman Usman ne ya sanar da hana mabiya Shi’a gudanar da zanga-zanga a jihar domin gudun kada ya tada da zaune tsaye.

Bayan haka Ibrahim Musa ya ce hana su tafiyyar da aiyukkan su da gwamantin jihar Sokoto ke kokarin yi karya dokar kasa ce wanda ta baiwa kowa damar shiga kungiyar da yake so sannan ya kuma da ‘yancin gudanar da zanga-zanga.

Ya kuma kara da cewa kungiyarsu bata gudanar da zanga-zangan da zai tada rikici domin hakan ba shine koyarwan shugaban su Ibrahim El-Zakzaky ba.

Daga karshe ya ce bisa ga yancin da dokar kasan ta basu kungiyar zata gudanar da zanga-zanganar a jihar Sokoto da kuma sauran bangarorin kasarnan.

Share.

game da Author