TSOHO YA SAUKA DA KWARI: Abubuwa 15 da Buhari yayi cikin kwanaki 42 da dawowarsa

0

1 – Duk Ma’aikatun gwamnati sun kammala shirya ababen da suke bukata a kasafin Kudin 2018.

2 – Amincewa duk jihar da take so ta karbi titunan da ke karkashin gwamnatin Tarayya ta rubuto, za’ a yardan mata.

3 – Mika Shirin gwamnati na bunkasa tattalin arzikin kasa ba ta hanyar mai ba, in da za a maida hankali wajen bunkasa ayyukan gona in da sama da matasa 500,000 zasu sami aikin yi.

4 – Kaddamar da shirin samar wa biranen kasarnan ruwan sha.

5 – Karbar rahoton kwamitin binciken zargin harkallar kwangilar datse ciyawa da ake yi wa Sakataren Gwamnatin Tarayya, wanda aka dakatar.

6 – karbar sakamakon binciken harkallar tulin kudin da aka kama a wani gida a Legas, wanda binciken ya shafi Daraktan Jami’an Tsaro na Leken Asiri.

7 – Buhari ya ci gaba da fitowa karbar manyan baki daga kasashen waje kuma ya karbi shugabannin kasashe.

8 – Tafiyar sa Daura domin hutun Babbar Sallah, shi ma wani abu ne da ke nuna cewa lallai ya samu sauki. Domin shagalin bikin Sallah abu ne na cudanya da jama’a masu dimbin ya wa da za su rika kawo ziyarar gaisuwa.

9 – Zanga-zangar kungiyoyin kwadago, malaman jami’o’i, ma’aikatan jami’o’i da kuma malaman asibiti ba ta girgiza shi har ya sake bukatar ganin likita ba domin zuwa yanzu har an daidaita da kusan dukkan su, kuma gwamnati ta ci gaba da aiki.

10 – Babbar rawar da Buhari ya taka bayan dawowar sa, ita ce murkushe ‘yan taratsin IPOB, masu so su kafa Biafra. An shafe shekara biyu shugaban kungiyar Nnamdi Kanu na barazanar yamutsa Najeriya domin ta watse, kowa ya kama gaban sa. Shi kan sa Buhari ya sha zagi na cin mutunci daga bakin Nnamdi Kanu.

A yau babu Nnamdi Kanu, babu tutocin su, kuma babu sauran wani tsagera mai yawo kan titi ya na hauragiya. Su kan su sojojin baka da ‘yan taratsin Biafra a Facebook da sauran kafafe na soshiyal midiya, sun yi tsit. Wadanda ke alakanta shafukan su na Twitter, Instagram, WhatsApp da Facebook su na lika tutar Biafra, duk sun cire.

11 – Buhari ya yi ‘yan tafiye-tafiye a cikin gida, ciki kuwa har da zuwa kaddamarwa ko bude kamfanin sarrafa abincin kaji da na dabbobi a Kaduna.

12 – Wata babbar nasara kuma ita ce halartar da Shugaba Buhari ya yi a taron Majalisar Dinkin Duniya, a birnin New York na Amurka. A wurin taron, karsashi, tasiri da kimar Buhari ta karu. Sannan kuma ya yi jawabin da dimbin masoyan sa ke ganin alama ce ta kankaro Najeriya da kuma Afrika a idon duniya.
Jawabin Buhari a wurin ya kara wa jama’a kwarin-guiwar cewa to tsoho fa dai ashe ya sauka da kwari. Idan aka kwatanta da jawabin sa bayan dawowa daga Landan, su kan su masu adawa sun san jiki dai ya kara murmurewa.

13 – Buhari ya yi namijin kokarin ganin ya biya ma’aikatan hukumar jiragen sama ta Nijeriya hakkin da su ke bi sama da shekara goma, kudin da sun zarce bilyan 200, wadanda gwamnatocin baya su ka gaza bilyan su.

14 – Zare idanun da Buhari ya yi wa gwamnoni masu taurin biyan ma’aikata albashi da sauran kudaden su, ya nuna cewa Shugaba Buhari da karfin sa ya dawo.

15 – Ci gaba da damke wadanda ake zargi da wawure dukikar kasar nan, ya tabbatar da cewa shugaban ba da wasa ya ke yi ba a jawabin sa bayan dawowar sa, inda ya ce ba zai sassauta ba daga himmar sa ta taka ruwan cikin duk wanda ya ci buzun Najeriya, domin ya wo aman gashi.

Share.

game da Author