Tsohon gwamnan jihar Anambra Peter Obi ya ce in banda hasara da rashin sanin inda aka dosa a kasar nan babu wani ci gaba ko nasara da aka samu tun da Buhari ya zama shugaban kasa.
Peter Obi ya fadi haka ne a wajen taron bunkasa tattalin arzikin jihar Ebonyi da akayi yau a Abakaliki.
Ya ce kasarnan har yanzu ana mulkinta ne kamar shugabannin yan koyo ne. Babu wani hikima cikin jagorancinsu.
” Idan dai wannan mulki ne na Buhari, ka gaya ma kowa cewa ba a samu wani ci gaba ba tun da aka rantsar da ita. Sai dai ma lalata kasar da tayi.
” Kuma bari in gaya muku wani abu kiranye kiranyen da ake tayi na araba kasa, yanzu ma aka fara.
Ya ce dukka shirye shiryen gwamnati shirye shirye ne da ba a amfani dasu yanzu. Kamar hako ma’adanai da sauransu. Ya ce duk shiri ne da duniya ta wuce su.
” Sannan duk wanda ya ce maka wai an fice daga tabarbarewar tattalin arzikin a Najeriya, ka ce mishi karya ne. Mutane na na na wahala.