Jihar Sokoto ta ba da hutun shiga sabuwar shekarar musulunci

0

Gwamnatin jihar Sokoto ta bada hutu gobe Juma’a don murna shiga sabuwar shekarar musulunci.

Gwamnan jihar Aminu Tambuwal ne ya sanar da haka ta hannun kakakinsa Imam Imam.

Gwamnan ya yi kira ga mutanen jihar da su yi amfani da hutun wajen yi wa jihar da kasa Najeriya Addu’a.

Jiya jihohin Osun da Kano suma suka sanar da hakan a jihohinsu.

Share.

game da Author