Majalisar Tarayya ba ta umarci EFCC ta bude wa Patience Jonathan asusun bankunan ta ba -Inji Hon. Gbajabiamila

0

Majalisar Tarayya ta musanta rahoton da aka yada cewa ta umarci hukumar EFCC da bankuna su bude wa Patience Jonathan asusun ajiyar kudaden ta.

Shugaban Masu Rinjaye, Femi Gbajabiamila ne ya bayyana haka Daren jiya a shafin sa na Twitter, ya na cewa rahoton ba gaskiya ba ne.

Rahoton dai ya bayyana ne inda aka ruwaito shugaban kwamitin sauraren koke-koke da kararrakin jama’a, Hon. Uzoma Nken daga jihar Abia ta bayar cewa ta na umartar bankuna 6 wadanda EFCC ta kulle Asusun ajiyar matar tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan da su gaggauta bude mata abin ta.

Ganin wannan rahoto, sai Hon. Gbajabiamila ya garzaya shafin sa na Twitter, ya bayyana cewa majalisa ba ta bayar da wannan umarni ga bankunan ko kuma EFCC ba.

Ya ce kwamitin dai ya kammala aikin sa, kuma sai majalisa ta koma bayan hutu ne za ta tattauna rahoton na Hon. Uzoma.

EFCC na rike da asusun bankunan Patience Jonathan, har guda shida a bankuna daban daban. Baya ga makudan kudaden wadanda EFCC ta rike, akwai kuma maka-makan kadarori da aka kwace, wadanda ake bincike kan yadda ta mallake su.

Share.

game da Author