Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a, JAMB, ta bayyana cewa ta shigo da sabon tsari ne na shiga jami’a domin ya inganta cin gashin kan kowace jami’a.
Tsarin a cewar hukumar zai tabbatar da ana yi wa masu neman shiga jami’o’i adalci musamman na yawaitar samun karin guraben yin ilmi, sannan kuma kalandar shekarar karatu ta rika tafiya daidai da ta sauran kasashe.
Rijistara na hukumar, Ishaq Oloyede ne ya bayyana haka ranar Alhamis a Abuja, yayin da ake jawabi a wurin taron bada horo da wayar da kai na 2017/2018.
Oloyede, ya bayyana cewa rashin yawan guraben dalibai a jami’o’in kasar nan ne ya sa tilas ake shirya jarabawar shiga jami’o’i ta UTME, har ta kai jarabawar ta zama tilas.
Ya ce hukumar JAMB ita hukuma ce da ke dora jami’o’i a kan sikelin yanayi, nagarta da zurfin bayar da karatun su, ba hukuma ce ta shirya wa dalibai jarabawa kamar WAEC, NECO da NABTEB ba. Dalili kenan inji ya ce JAMB ba ta bayar da satifiket.
Oloyede ya yi tir da yadda wasu jami’o’i ke daukar dalibai fiye da yadda ka’ida ta ce a dauka.
Da ya ke magana a kan muhimmancin jarabawa, sai ya kara da cewa hukumar sa ba za ta yarda wani dalibi ya zarce jami’a ba, har sai ya ci jarabawar ‘O levels da ‘A levels.
A kan kokarin da ya yi wajen tara har naira biliyan 5 a matsayin riba ga gwamnatin tarayya, wanda su ne adadi mafi yawa da aka taba tara wa gwamnati, sai farfesan ya ce “ai abin kishi ne”, kuma a jiki da jinin sa kishin ya ke na ganin cewa ya tara wa gwamnati abin da ya dace ya tara mata.
“Ni dan Najeriya ne, kuma ina alfahari da kuma biyayya ga kasa ta.” Inji shi.
Discussion about this post