Gamaiyar kungiyoyin likitoci da na ma’aikatan asibiti ta yi barazanar rufe asibitocin kasar nan

0

Yayin da gwamnati ke ta kokarin shawo kan likitoci su janye yajin aiki, Gamaiyar kungiyoyin likitoci da na ma’aikatan asibiti sun shigo cikin yajin aikin har ta na barazanar rufe asibitocin kasar nan.

Gamaiyar Kungiyoyin mai lakabi da JOHESU, ta ce sun yi shirin fara yajin aiki a ranar 20 Ga Satumba, 2017.

Ta ce sun yanke shawarar tafiya yajin aiki ne saboda gwamnati ta ki biya musu dukkan bukatun su.

Kungiyar dai a baya ta taba yin barazanar tafiya yajin aiki na dindindin ta yadda babu yadda za a yi, sai dai a rufe asibitocin kasar nan baki daya.

Hakan inji ta, ya faru ne sakamakon lattin da gwamnatin tarayya ta yi na kasa biya musu bukatun su tun na cikin 2014. Daga cikin abin da su ka nema a hannun gwamnatin tarayya, sun hada da biyan su kudaden ariyas, kudaden alawus na ayyukan musamman da kuma gaggauta karin girma da mukamai ga mambobin su wadanda su ka cancanta ko su ka kai shekarun yi musu karin.

JOHESU dai ta kira wannan yajin aiki da za ta fara da suna ‘Cizon Kada’, tare da gargadin cewa yajin aikin na su zai fi aikin da sojoji za su yi a kudu-maso-gabas radadi, wato shirin nan na ‘Rawar Kumurci’ da sojoji za su fara da nufin dakile tsagerancin ’yan Biafra.

Wannan barazana ta zo kwanaki takwas kacal bayan kungiyar likitoci ta Najeriya ta faara yajin aiki.

Share.

game da Author