Kada ‘yan Arewa su rama tsokanar da tsagerun ‘Biafra’ ke mana -Inji Kungiyar Matasan Arewa

0

Kungiyar Matasan Arewa da aka fi sani da Northern Youth Coalition, ta yi kira ga daukacin ‘yan Arewa a da su daure, kada su kula da irin takalar fadan da tsagerun Biafra key i wa ‘yan Arewa.

Kungiyar dai a can baya ta taba bayar da sanarwar wa’adi ga daukacin ‘yan kabailar Igbo da su kwashe komatsan su su koma yankin Kudu-maso-gabas.

Matasan sun yi wannan sanarwar juriyar kada a maida martani ne a yau Laraba, a Cibiyar ‘Yan Jarida ta Kano. Ta ce kungiyar ta gano cewa gaba dayan iyashege da rashin kunyar da ake yi yankunan jihohin Igbo, du kana yi ne don a tsokani ‘yan Arewa rigima, kasar ta dagule baki daya.

Kakakin kungiyar Abdul’Aziz Suleiman ya ce “duk wannan tashe-tashen hankulan da suke yi fa sun tsara shi ne don kasar nan ta dagule nan da 2019, da nufin a samu dalilin faduwar gwamnatin Buhari, ta yadda zaben ma ba zai yiwu ba.”

Ya na mai cewa, “ya na da kyau mu a nan Arewa mu nuna kawaici kada mu kula su ko yin wata ramuwar gayya, wanda idan aka yi ramuwar gayya, to bukatar su ta hargitsa kasar nan ta biya kenan.

“Irin yadda su ke zakalkalewa su na cewa sai sun kai wa Buhari hari ai wata hila ce da nufin jawo sabon rikici tsakanin yankin Arewa da Kudu-maso-gabas.” Inji Abdul’Aziz.

Sauran wadanda suka halarci taron, sun hada da Yarima Shatima da Mustara Sharif, sun kuma yaba wa Gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu, dangane da dokar-ta-baci da ya kakaba a jihar. Sun kuma nuna goyon bayan su dangane da tura sojoji da gwamnatin tarayya ta yi a yankin.

Share.

game da Author