Gwamnatin Yobe za ta gina tashar jirgin saman manyan Kaya a Damaturu

0

Kwamishinan ilimi na jihar Yobe Mohammed Lamin ya ce gwamnatin jihar ta ware Naira biliyan 11.32 musamman domin gina tashar jirgin sama don jigilar mayan kaya a garin Damaturu.

Mohammed Lamin ya fadi hakan ne wa manema labara ranar Laraba.

Ya ce tashar za ta yi jigilan kayayyaki daga ciki da wajan jihar.

Mohammed Lamin yace jihar tayi haka ne domin ta kara samun kudaden shiga da kuma bunkasa tattalin arzikin jihar.

Ya kuma kara da cewa gwamnatin ta ware Naira miliyan 440.27 domin siyo kujeru da gadaje saboda ofisoshi, ajujuwa, gidajen malammai da dakunan kwana na makarantu biyar da jihar ta gyara.

Ya ce gwamnatin ta bada Naira miliyan 99.9 domin siyo motoci biyu (buses) wa kwalejin horar da ma’aikatan jinya da unguwan zoma.

‘‘Gwamnatin za ta gyara makarantan firamare a Bayamari domin ya zama kwalejin horar da yara zuwa sojin kasa da Naira miliyan 238.76’’.

Share.

game da Author