Dole Atiku yayi takatsantsan sannan Aisha kuma ta sauka daga kujeran minista – Inuwa

2

Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na yankin Arewa maso Yamma, Inuwa AbdulKadir ya ce maganganun da Aisha Alhassan tayi kan mara wa tsohon mataimakin shugaban kasaAtiku Abubakar baya a 2019 bai da ce ba.

Inuwa ya ce bai kamata ace wai a matsayin ta na minista a wannan gwamnati kuma ta fito karara ta nuna cewa ba za tayi wanda take wa aiki ba a 2019.

” Da ma can Aisha ba ta tare da Buhari, saboda haka abin da ta fada bai bani mamaki ba.

Inuwa Abdulkadir yayi kira ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da ya zamo mutum mai dattaku da sanin ya kamat musamman ganin cewa yanzu ya shiga sahun dattawa.

” Dole ne ya dinga kimanta irin maganganun da zai fadi saboda matsayinsa a kasa. Duk abin da zai ce zai yi tasiri a zukatan mutanen sannan fadiin irin maganganun da yakeyi ba dace da shi ba.”

Ya kara da cewa hakan zai iya kawo rarrabuwa a jam’iyyar sanna ita kuma Aisha Alhassan ta yi wa kanta kiyamun laili ta yi murabus.

Share.

game da Author