Plateau United ta lashe kofin zakarun gasar kwallon kafa ta kasa

0

Kungiyar Kwallon Kafa ta Plateau United da ke Jos, ta zama zakaran gasar Premier League na Najeriya ta 2017. A wasan karshe da ta buga a filin wasa na garin Jos, ta yi nasara a kan kungiyar Enugu Rangers da ci 2:0.

Plateau United dai ta samu maki 66 daga cikin wasanni 38 da ta buga.

Baya ga kofin da aka damka wa ‘yan wasan kungiyar, an kuma ba su kyautar kudi har naira miliyan 50.

Plateau United da wacce ta zo ta biyu ne, wato kungiyar MFM za su wakilci Najeriya a gasar Zakarun Afrika.

A can kasa kuwa, an zabtare kungiyoyi hudu wadanda za a maida su Rukuni na Biyu, saboda rashin kokarin su.

Kungiyoyin hudu su ne: Shooting Stars, ABS ta Ilorin, Gombe United da kuma Remo Stars.

AN TASHI WASA BA SHIRI A GOMBE

Sai kuma rahotanni daga Gombe sun tabbatar da cewa an tashi wasa tsakanin Gombe United da Wikki Tourists ba shiri, yayin da magoya bayan Gombe United su ka tayar da hargitsi.

Magoya bayan sun fusata ne yayin da mai tsaron bayan kungiyar, Morris Chigozie ya antaya kwallo a cikin ragar su da kan sa, abin da aka fi sani da ‘own goal.’

Hasalallun magoya bayan kungiyar sun yi zargin cewa da gangan Morris Chigozie ya jefa kwallo a raga. Sun yi ikirarin butulce wa Gombe United ya yi, inda ya hada baki da Wikki Tourists domin su yi nasarar tsallake wa komawa rukuni na biyu.

Alkalin wasa dai ya tashi wasan tun kafin lokacin tashi ya yi, kasancewa kowa na ran sa.

Share.

game da Author