Gwamnatin jihar Katsina ta kara wa malaman makarantan firamare 19,600 girma don karfafa musu guiwa da bunkasa fanin ilimi a jihar.
Jami’i a hukumar bada ilimi a matakin farko na jihar, (SUBEB) Lawal Buhari ne ya sanarwa kamfanin dillancin labaran Najeriya hakan ranar Juma’a a Daura.
Ya ce sun kara wa malaman firamaren girma da suka cancanta daga shekarun 2013 zuwa 2015 sannan sun fara shirye-shiryen kara girman sauran malaman daga da aka dauka daga shekarar bara zuwa bana.
Lawal yace gwamnatin jihar na shirin daukan sabbin malamai 1,900 domin kara yawan malaman jihar.
Ya kara da cewa za su dauki sabbin malaman ne daga kananan hukumomin 34 dake jihar.
Bayan hakan gwamantin jihar Katsina ta samar da kayayyakin koyarwa a makarantun jihar da suka kai Naira miliyan 600.