Irin alfanun da kudin da aka kwato daga Diezani za su yi wa Najeriya

0

Wata kungiyar kare manufofin Shugaba Muhammadu Buhari, mai suna Buhari Media Support Group, ta bayyana irin dimbin ayyukan raya kasa da inganta al’umma da za a iya yi da makudan bilyoyin kudaden da aka karbo daga Diezani Allison-Maduekwe.

Maduekwe ita ce ministar man fetur a lokacin gwamnatin Goodluck Jonathan, wacce ake zargin ta da sace dukiya malala gashin tinkiya, wasu ma na cewa fan-cika-teku.

Shugaban kungiyar Austin Braimoh da Sakataren sa Cassidy Madueke, sun bayyana cewa za a iya gina manyan filayen sauka da tashin jiragen sama irin wadanda duniya ke tinkaho da su, har guda shida.

Haka dai kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito daga gare su.

Sun kuma kara da cewa a cikin kudaden za a iya aiwatar da gagarimin shirin ingata mona a kasar nan, wanda zai iya samar wa dubun dubatar matasa aikin yi.

Har ila yau, sun kara da nunin cewa daga cikin naira bilyaN 42.7 da kuma Dala milyan 487.5 na zunzurutun kudaden da EFCC ta gano a hannun ta, za a iya karasa aikin titin jirgin kasa daga Lagos zuwa Kano da kuma Lagos zuwa Calabar.

Kungiyar ta kuma yi kira ga daukacin ‘yan Nijeriya da su fito su yi tir da Allah wadai da wadanda su ka warure kudin talakawa a gwamnatin da ta gabata.

Kungiyar ta kuma ce irin makudan miliyoyin Dalolin da aka sace a gwamnatin da ta gabata, hakan ne ya jefa kasar nan cikin mawuyacin halin da aka tsinci kai a ciki yanzu.

Sun kuma tunatar da ‘yan Najeriya cewa Diezani da abokan harkallar ta su Kola Aluko da Jide Omokore a yanzu haka su na fuskantar shari’a da tuhumar harkallar kudade a Amurka.

Share.

game da Author