Babban lauya Femi Falana, ya bayyana cewa ya zama dole gwamnatocin jhohi su tashi su kalubalanci dokar da ta ce ba zu samar wa kan su hasken lantarki da sauran nau’ukan makamashi ba.
Lauyan ya na magana ne yayin daa ya ke gabatar da jawabi da wani taro da kungiyar sa’ido da kuma tabbatar da yin ayyuka kan gaskiya, da aka fi sani da SERAP, wanda aka gudanar a ranar Laraba a Lagos.
Takardar ta sa mai taken: “Daga duhu zuwa duzu, ta yi tsokaci ne kan yadda harkalla da rashawa da cin hanci su ka dabaibaye tsarin samar da wutar lantarki, aka bar talakawa a cikin duhu, shekara da shekaru.
Gidauniyar bayar da tallafi ta McArthur Foundation ce ta shirya gudanar da taron.
Falana ya ce dole gwamnatocin jihohi su tashi su nuna ‘yancin su na kalubalantar kankane harkar lantarki da makamashi da gwamnatin tarayya ta yi.
Ya yi nuni karara da wasu ayoyi biyu na 13 da na 14, a cikin dokar samar da lantarki, wadanda ke nuni da cewa jihohi ma sun a da ikon samar wa kan su harken lantarki.
“Dokar ta ci gaba da cewa Majalisun Jihohi za su iya kafa doka a kowace jiha domin si samar da lantarki.
“Ni ke samar wa kai na lantarki a gida na, haka a ofis. To don me gwamnan jihar Lagos ba zai iya samar da lantarki gare mu ba – mu da mu ka kai adadin milyan 20?