Boko Haram sun yi mummunan kisa, sun kona gidaje 60 a Adamawa

0

Ana zaton cewa Boko Haram sun kashe mutane da dama, bayan kone gidaje 60 a wani harin baya-bayan nan da su ka kai a Ghumbili, cikin Karamar Hukumar Madagali da ke Jihar Adamawa.

Wannan hari ya afku ne, kwanaki kadan bayan wani hari a gari mafi kusa da kauyen, mai suna Mildu, wanda ya haifar sa asarar rayukan mutane bakwai.

Da ya ke tabbatar da harin, shugaban karamar hukumar Madagali, Yusuf Muhammad, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai , NAN, cewa Boko Haram sun shafe sa’o’i hudu su na kaddamamr da hare-haren , tsakanin 11 na dare har zuwa 3 na asubahi.

“Sun kona gidaje 60, sun kashe mutane da dabbobi.” Inji shi shugaban karamar hukumar.

Muhammada ya ce ba zai iya tantacen yawan wadanda aka kashe ba, amma dai ya ce wadanda suka tsira da ransu, duk su na sansanin ‘yan gudun hijira da ke Gulak.

Sai dai kuma kakakin rundunar ’yan sandan jihar Adamawa Othman Abubakar, ya ce ya samu rahoton kai harin, amma babu wanda ya rasa ran sa.

Share.

game da Author