‘Yan siyasa na amfani da jami’an tsaro wajen muzguna wa ‘yan Jarida – NUJ

0

Wani dan jarida a jihar Katsina ya gamu da wulakancin ‘yan siyasa inda saboda fadin ra’ayinsa da yayi a shafinsa na Facebook game da zaben da akayi a jihar ya kaishi ga kwana a caji ofis.

Dan jaridan mai suna Danjuma Katsina ya rubuta rashin cancantar dan majalisar da ya lashe zaben cika gurbin kujerar dan majalisar Wakilai na kananan hukumomin Mashi/Dutsi da akayi a jihar.

Duk da kokarin da kungiyar NUJ ta yi don ganin ba a ci gaba da tsare shi ba hakan ya ci tura domin yan sandan sun ci gaba da tsare shi.

A jihar Kaduna an yi amfani da makaman iko wajen muzguna wa ‘yan Jarida inda kungiyar NUJ ta gargadi gwamnatin El-Rufai akan haka a wata sanarwa da ta fitar a makon da ya gabata.

Haka kuma akwai wani dan jarida da aka tsare har tsawon kwanaki 22 a jihar Bauchi shima duk saboda irin haka.

Share.

game da Author