Abubuwa 8 da za a kiyaye don gujewa kamuwa da cutar Kwalera

0

Gwamnatin tarayya ta yi kira ga mutanen da su mai da hankali waje tsaftace muhallin su da ruwan da za su shan domin gujewa kamuwa da cutar kwalera.

Gwamnatin ta fadi hanyoyi da za a iya bi domin samun kariya daga kamuwa da cutar kamar haka;

1. A tsaftace ruwan sha ta hanyar tafasa ruwa sanna a tace shi ko kuma a zuba sinadarin dake tsaftace ruwa wanda ake kira da ‘Chlorine’.

2. A yi amfani da tsaftattacen ruwa wajen wanke ido da hakora.

3. A girka abincin da tsaftacen ruwa.

4. Wanke hannu kafin da bayan an ci abinci musamman ga yara kanana.

5. Idan ana jinyar wanda ya kamu da cutar kwaleran a tabbatar an wanke hannu bayan an gama duba shi.

6. A daina yin bahaya a fili, sannna a yawaita wanke bandakin akai- akai sannan kuma bayan an gama amfani da bandakin a tabbatar an wanke hannu da ruwa da sabulu.

7. A daina wanke wanke ko wankin kaya a kusa da inda a ke diban ruwa kamar su rijiya ko kuma fanfo.

8. A nisanta bandaki daga wajen da mutane ke zama musamman wajen da ake ajiye ruwan sha.

Bayan haka hukumar kula da hana yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta yi kira da a isarwa mutanen dake zaune a karkara wannan sako.

Share.

game da Author