Wata kotu a Zariya, jihar Kaduna ta gargadi gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai da kada ya kuskura ya ci gaba da shirinsa na rusa masarauutun jihar da ya sanar.
Alkalin Kotun Maishari’a BF Zubairu y ace dole gwamnati ta dakatar da wannan shiri nata har sai an gama sauraren karar da aka shigar a kotunan jihar kan hakan.
Wannan dai shine karo na biyu da kotu a jihar ke dakatar da gwamnan daga ci gaba da wannan shiri na gwamnatin Jihar.
Gwamnatin El-Rufai ta sanar da rusa masarautu sama da 4000 da aka kirkiro a jihar a shekarar 2001.
Hakimai Uku ne suka shigar da karar a kotu.