Gwamnatin jihar Kano ta canza sunar jami’ar Northwest mallakar jihar zuwa jami’ar Maitamat Sule.
Gwamnatin ta sanar da haka ne bayan wata mitin na gaggawa da ta yi jiya a garin Kano.
Bayan canja sunan jami’ar Northwest da ta amince da shi an canza sunan titin Dawaki dake cikin birnin Kano zuwa titin Yusuf Maitama Sule.