Tsohon gwamnan jihar Cross River Donald Duke ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta raba ikon da rundunar ‘yan sanda ke da shi sannan kuma a hana ‘yan sandar zaman bariki.
Ya fadi haka ne da yake tofa albarkacin bakinsa a taron kaddamar da wata takarda mai taken ‘Mahimmancin doka akan kawar da gano miyagun aiyukka ga dan sanda a Najeriya’.
A jawabinsa fadi wasu matakai biyar da za su taimaka wajen bunkasa aiyukkan ‘yan sanda a Najeriya kamar haka;
1. Raba ikon da rundunan ‘yan sanda ke da shi zai taimaka wajen kawar miyagun aiyukka.
2. A yawaita gudanar da jarabawa ‘Aptitude Test’ a lokacin daukan sabobin ma’aikata da kuma lokacin karin matsayi wa ‘yan sandan sannan ya kamata masu babbar Diploma ne za a dauka aikin dan sandan.
3. Horas da ‘yan sandan akai akai musamman wanda ya shafi dabarun tsaro na zamani.
4. A hana ‘yan sanda zaman bariki saboda ya kamata su zauna tsakin mutanen da suke karewa.
5. A daina ko kuma a rage yadda ake tura jami’an ‘yan sanda daga wani bangaren kasar zuwan wasu.