Dalilin da ya sa muka dakatar da kamfanin Atiku (Intels’) – Hadiza Bala Usman

1

Shugaban hukumar tashoshin ruwan Najeriya (NPA) Hadiza Bala Usman ta fadi wasu dalilan da ya sa hukumar ta dakatar da kamfanin Intels’ wanda mallakin tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya ne Atiku Abubakar daga ci gaba da more iko da take dashi na aiki ita kadai a tashoshin ruwar kasar.

Ta ce anyi haka ne domin ba wasu kamfanoni damar gudanar da irin ayyukan da kamfanin intels’ din ke yi a tashoshin ruwan.

Hadiza ta fadi haka ne a wata hira da tayi da gidan Jaridar Daily Trust.

Ta ce hukumar tashoshin ruwan ba ta yi haka ba don ta muzguna wa kamfanin Intels’ cewa ta yi haka ne domin kowa ya samu damar shiga harkar dako da adana mai da iskar gas a tashoshin kasar mai makon barin kamfanin Intels’ din tana cin karenta ba babbaka.

Da aka tambayeta game da zargi da ake yi cewa hukumar ta yi hakane don dakile hanyoyin samun kudinsa saboda hanashi takarar shugaban kasa a 2019, Hadiza ta ce wannan maganar kanzon kurege ne amma ba haka suke nufi ba da dakatar da kamfanin Intels’.

Ta ce har zuwa lokacin da aka dakatar da kamfanin Intels kamfanin ba ta bude asusun nan na bai daya da kowace ma’aikata ta koma wato TSA. “ Idan aka tuntube kamfanin kan haka sai ta ce za ta yi amma shiru. Sannan kuma shugaban kasa da kansa ya umurce mu da a sakar wa kowa ikon iya gudanar da aiki a tasshoshin ruwar kasar.”

Share.

game da Author