Ba Giriringirin Ba: Nasarori a matsalolin nasarar Makarfi a kan Sheriff

0

Nasarar da Sanata Ahmed Mohammed Makarfi ya samu a kan Sanata Ali Madu Sheriff inda Kotun Koli ta damka masa shugabancin jam’iyyar PDP, ya sa jama’a da dama na yi wa abin fassara daban-daban. PREMIUM TIMES HAUSA ta kalli hukuncin kotun ta bangarori da dama kamar yadda za a karanta daki-daki:

Nasarori

1 – Makarfi ya samu nasarar a daidai lokacin da mafi yawan gaggan jam’iyyar PDP ke tunanin kafa sabuwar jam’iyya matukar aka damka shugabanci ga Modu Sheriff. Don haka Makarfi na da goyon bayan PDP fiye da Sheriff.

2 – Wannan hukunci da Kotun Koli ta zartas ya farfado da ruhin da yawan mambobin jam’iyyar wadanda yawancin su jikin su ya yi sanyi, wasu kuma sun suma, tun bayan da su ka sha kaye a zaben 2014.

3 – Da yawan wadanda su ka sa wa bakin su takunkumin magana tun bayan faduwa zabe, sun samu bakin magana har su na kartar kasar fara shirin kokawar neman kayar da APC a zaben 2019.

4 – Wata nasarar da Makarfi ko PDP ta samu, shi ne ganin yadda manyan jiga-jigan PDP na yankin Kudu-maso Gabas da kuma Kudu-maso-Yamma su ka yi cincirindon mara wa Makarfi baya, a kotu da kuma sakateriyar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja. Hakan na nufin kenan masu cizon baki su na zara idanun su “ko-Biyafara-ko-a-mutu, ba za su samu goyon bayan manyan su ba.”

5 – Gaggan PDP irin su Gwamnan Jihar Ribas Nyesome Wike da Ayo Fayose na Jihar Ekiti, zun zakalkale sosai wajen nuna adawa ga Sheriff, hakan na nuni da cewa hankulan manyan ‘yan PDPin kudancin kasar nan, ya karkata ne ga zaben 2019, ba su damu masu neman a raba Najeriya ba.

Matsaloli

1 – Duk da cewa jam’iyyar APC na cikin rudani, sannan kuma al’umma na dandana rayuwa mai tsadar gaske tun bayan hawa mulkin APC, har yanzu ana ganin cewa PDP ce silar shiga wannan matsala.

2 – Arewa, har yau wasu da ake kallon su ne a sahun gaba wajen wawure dukiyar jama’a a lokacin mulkin PDP, sun kasa fitowa su yi wandaka su yi warisa a cikin jama’a, saboda tsangwamar da ake yi musu.

3 – Shi kan sa Sanata Makarfi ba shi da gogewar fitowa ya na yin gumurzu da gomozo da zaratan yan siyasar Arewacin kasar nan, inda daga nan ne ya fito. Ko a Kaduna ma, ba a cika jin zakaran sa na cara da asubahi ko da rana tsaka ba. Sannan kuma da alamu har yanzu kamar Sheriff bai hakura ba, ta-ciki-na-ciki, watakila zai iya yi wa PDP tadiya.

4 – Har yanzu PDP a Arewa ba ta da fikafikan yin faffaka sosai, kamar yadda ta ke yi a kudancin kasar nan. Babban jigon ta Namadi Sambo, shiru kamar ruwa ya ci biri. Zakakurai irin su tsohon gwamna Shema kuwa, har yau su na kokarin kubcewa daga kamun-kazar-kukun da EFCC ta yi musu. Masu baki irin su tsohon gwamnan Neja Aliyu kuwa, za a iya cewa kaji sun kare sun bar sa.

5 – Idan ka debe tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, wanda a yanzu shi kadai ne za a iya cewa ruhin PDP a Arewa, babu masu fitowa gaba-gadi su na kare jam’iyyar daga sara da sassakar da ‘yan APC ke yi mata. Dalili kenan masu lura da siyasar kasar nan ke cewa Lamido ne kadai zai iya fitowa ya daura banten kokawar yaki da APC har kila ya yi nasara a 2019.

Baya ga wannan, irin yadda mutane irin su Femi-Fani Kayode ke zagin ‘yan Arewa muraran a kafafen yada labarai, hakan zai iya zama tangarda ga PDP a Arewa, muddin ba a yi hanzarin taka masa burki ba.

Share.

game da Author