Shugaban hukumar kula da aikin hajji ta kasa (NAHCON) Abdullahi Mohammed ya ce mutane 50,000 ne suka kamala biyan kudin aikin hajjin su zuwa yanzu.
Abdullahi ya fadi haka ne a wani taron masayan ra’ayi da hukumar ta shirya.
Bayan haka yayi kira ‘yan jarida da su bada rahoton gaskiya kan abubuwan da hukumar ke gudanarwa saboda mahimmancin aikin hajji.
Maniyyata 97,000 ake kyautata zaton za su gudanar da aikin bana.
Jihar Kaduna ce ta fi yawan maniyyata a bana.