Kungiyar masu fafutukar neman kafa kasar Biafra, MASSOB ta yi kira ga ‘yan Kabilar Igbo da ke zaune a Arewacin Najeriya da su fara shirin dawowa gida.
Shugaban kungiyar Uche Madu ya ce kowani dan Kabilar Igbo ya tattara kayansa da dawo su gina yankinsu na Biafra.
Ya ce dama wannan shiri ne da shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi tare da jam’iyyarsa na APC don muzgunawa kabilar Igbo a kasar.
Duk da cewa gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya umurci jami’an tsaro da su kamo shugabannin wadannan kungiyoyi sannan ma’aikatar shari’ar jihar ta shigar da kara akan hakan, MASSOB ta ce duk da hadin bakin shugabannin yankin Arewan.
Sakataren kungiyar Ohaneze Uche Achi-Okpaga ya roki ‘yan Kabilar Igbo din da su zauna da kowa lafiya sai dai kuma idan suka ga cewa ana yi wa rayuwarsu barazana to mutum ya dawo gida.
MASSOB ta ce babu abin da zai dakatar dasu daga neman kasarsu ta Biafra kuma hakan ya sa cikin ‘yan Arewa ya duri ruwa ne bayan ganin yadda suka yi zaman kwanaki uku na nuna juyayi shekaru 50 da kafa Biafra.
Uche Madu yayi kira ga ‘yan uwansa ‘yan Kabilar Igbo da su dawo yankinsu domin gina ta.
Gwamnann jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya umurci jami’an tsaron Jihar da su kama duk wanda ya sa hannu a takardar da wasu kungiyoyin matasa na yankin Arewa sukayi suna umurtar duk wani dan kabilar Igbo ya tattara inashi-inashi ya koma garinsu.
El-Rufai ya ce ya umurci ma’aikatar shari’ar jihar da lauyoyin jihar su shigar da kara akan wadannan matasa a kotu.
Ministan yada labara, Lai Mohammed yace mutane sun saba fadin irin wadannan maganganu a amma gwamnati ba za ta bari irin haka ya faru ba.
A wata sanarwa da hadaddiyar kungiyoyin matasan Arewa ACYF suka fitar sun ba duk wani dan kabilar Igbo da ke zama a yankin watanni uku da ya tattara inashi-inashi ya fice daga duk wani kusurwar na yankin Arewa.