A ranar Laraba ne gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta biyar masu fallasa inda aka boye kudin gwamnati ladar zunzururun kudi har naira milyan 375.8.
Wannan ladar a ta bakin Ma’aikatar Kudi ta tarayya, wanda aka fi sani da “whistleblower policy”, an raba kudin ne ga mutane 20, wadanda tonon sililin dà su ka yi ya harfar da gano kudi kimanin naira bilyan 11.6.
Wannan dai shi ne karon farko da aka fara biyan ‘ya-sa-ido tun bayan da aka kafa ta-baci ta whistleblower policy, dokar da ta amince cewa duk wani bayanin da ya haifar da fallasa kudaden da ‘yan siyasa da ma’aikatan gwamnati, to za a ba shi kashi biyar bisa 100 na kudin da aka kwato.
Ministar Harkokin Kudade ta bayyana cewa babbar fa’idar kafa dokar amincewa dabarar sa-ido, ita ce a kakkabe wawurar dukiyar jama’a da kula kula da baitilmali kwarai da gaske. Ta kuma yi kira da cewa duk wani mai labarin yadda aka kimshe dukiyar da aka wawura, to ya gabato ya fallasa domin a ci nasarar kwato hakkin jama’a da aka dade ana wawura.