El-Rufai ya umurci jami’an tsaro su kama mambobin kungiyoyin da suka yi wa kabilar Igbo barazanar korar su daga Arewa

0

Gwamnann jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya umurci jami’an tsaron Jihar da su kama duk wanda ya sa hannu a takardar da wasu kungiyoyin matasa na yankin Arewa sukayi suna umurtar duk wani dan kabilar Igbo ya tattara inashi-inashi ya koma garinsu.

El-Rufai ya ce ya umurci ma’aikatar shari’ar jihar da lauyoyin jihar su shigar da kara akan wadannan matasa a kotu.
Ministan yada labara, Lai Mohammed yace mutane sun saba fadin irin wadannan maganganu a amma gwamnati ba za ta bari irin haka ya faru ba.

A wata sanarwa da hadaddiyar kungiyoyin matasan Arewa ACYF suka fitar sun ba duk wani dan kabilar Igbo da ke zama a yankin watanni uku da ya tattara inashi-inashi ya fice daga duk wani kusurwar na yankin Arewa.

Bayan haka kuma kungiyoyin sun ce za mutanen arewa zasu karbi mallakin duk kaddarorin yan kabilar idan suka tashi.

Kungiyoyin sun ce sun gama shiri kaf kuma babu wanda zai hana su aiwatar da wannan shiri na su.

Shugaban Kungiyar ACYF, Yerima shettima ya ce ayyukan kungiyar Biafra musamman na kwana-kwanan nan inda suka umurci duk wani dan kabilar Ibo ya zauna a gida barazana ce ga kasa Najeriya.

“ Muna kira ga duk wani dan Arewa da yake yankin Kudu maso Gabas da ya fara shirin dawowa gida. Kowa ya dawo cikin wadannan watanni da muka ba da.

“ Abin da zamu fara yi bayan watanni uku da muka diba wa ‘yan kabilar Igbo ya cika shine mu mallaki duk wani abin da suka kafa a yankin Arewa.

Sannan kuma kungiyoyin sunce kada gwamnatin tarayya ta dauka wannan kira da su keyi wa ‘yan kabilar Ibo wasa ne.

Shugaban kungiyar Kabilar Igbo Ohaneze Ndigbo yayi kira ga jami’an tsaro da su tasa keyar Yerima saboda irin wannan kalamai da yayi kan ‘yan kabilarsa.

Ya yi kira ga jami’an tsaro da su tabbata sun bi diddigin wannan kalamai na barazana da ya fito daga kungiyar AYCF domin ba abin ayi masa burus bane.

Wadanda suka sa hannu a wannan sako sun hada da Nastura Ashir Sharif na (Arewa Citizens Action for Change); Alhaji Shettima Yerima na (Arewa Youth Consultative Forum); Aminu Adam na (Arewa Youth Development Foundation); Alfred Solomon na (Arewa Students Forum); Abdul-Azeez Suleiman na (Northern Emancipation Network), da kuma Joshua Viashman, wanda shine ya sa hannu a madadin kungiyar Northern Youth Vanguard.

Gwamnan jihar Kaduna yace Najeriya na kowa da kowa ne saboda haka ba zai sa ido ya ga wasu na neman muzguna wa mazauna garuruwar Arewar ba kuma ya ki daukar mataki akai.

Kakakin gwamnan, Samuel Aruwan ne ya saka hannu a wannan matsaya na gwamnatin jihar.

El-Rufai yace sun gana da shugabannin ‘yan kabilar Igbo a jihar kuma gwamnati ta sanar musu cewa su kwantar da hankalinsu.

Share.

game da Author