Shugaban kungiyar dattawan Arewa Farfesa Ango Abdullahi ya ce shi dai yana tare da kira da wasu kungiyoyin matasan Arewa su kayi wa ‘Yan kabilar Igbo da su tattara inasu-inasu su fice daga yankin Arewa.
Ango Abdulahi ya ce bai ga dalilin da zai sa gwamnonin Arewa su guji nasu ba bayan kiri-kiri ‘yan kabilar Igbo din ne suke nuna wa kowa a kasa Najeriya cewa su kasar su suke so wato Biafra kuma babu wani daga cikin gwamnonin yankin su da ya fito ya nuna cewa abin da suke yi ba daidai bane sai namu.
“ A gaskiya fitowa da gwamnonin Arewa suka yi karara don nuna adawarsu ga kungiyoyin matasan Arewa bai dace ba kuma bai yi mini dadi ba. Kiri-kiri sun fito sun nuna suna kyamar nasu.
Ango Abdullahi yace kwana-kwan nan ne mutanen yankin Igbo suka fito suka ci karensu ba babbaka kan fafutukar neman kasar Biafra da sukeyi amma babu wani gwamna a yankinsu da ya fito ya nuna hakan ba daidai bane ganin ana kasa daya. Haka kuma babu wani gwamnan Arewa da ya fito ya nuna cewa abinda suka yi ba daidai bane a lokacin sai gashi da ga yaran mu sun ce wulakancin da ake yi wa mutanen yankin ya isa haka duk sun fito suna ta maida musu da martini.
Ya ce Kungiyar dattawan Arewa na tare da matasan kuma za su basu duk irin goyon bayan da ya kamata domin cimma wannan buri.
Karanta labarin a shafin mu na Turanci: Igbo Quit Notice: Northern Elders Forum backs Arewa youth group
Discussion about this post