Majalisar Dinkin Duniya ta hori kabilun Najeriya da su kasancewa uwa daya uba daya

0

Majalisar Dinkin Duniya ta ja kunnen ‘yan Najeriya da su guji duk wata tashin- tashinar da za ta raba kan su har ta tarwatsa kasar daga kasancewar ta dunkulalliya daya.

Jami’in Majalisar ne da ke Nijeriya, Edward Kallon, ya yi wannan bayani a cikin wata takarda da ya fitar jiya Alhamis. Kallon ya fitar da jawabin ne sakamakon wani kalami da aka danganta da wata kungiyar matasan Arewa, da aka ruwaito cewa ta ba kabilar Igbo wa’adin watanni uku, zuwa 1Ga Oktorber, 2017 da su fice daga Arewacin kasar nan.

Ya ce ya nuna damuwar sa ne, dangane da wa’adin, wanda shi ma raddi ne a kan fartar kasar da matasan kabilar Ibo ke yi na neman kafa jamhuriyar su, wato Biafra, inda a ranar 30 Ga Mayu, 2017 suka yi sanarwar hana fita a yankin Kudu-maso-Gabas saboda jimamin tuna asarar da suka yi sakamakon yakin Basasa da aka yi a 1967 zuwa 1970.

“Kamata ya yi a ce mu na aiki tare, domin mu tabbatar da warware kowace iirin matsala ko korafin da kowane bangare ke yi.

“Kuma na ji dadi kwarai ganin yadda shugabanni daga bangarorin Najeriya da dama suka fito, suka yi tir da wancan wa’adi da matasan suka bayar.

“Don haka Majalisar Dinkin Duniya na kira da a daure a ci gaba da kasancewa tare a cikin girmamawa da fahimtar juna. Ta haka ne za a iya warware duk wata matsala domin kai ga cimma maslahar zamantakewa tare.”

Kallon ya kara da cewa Najeriya fa kasaitacciyar kasa ce, mai cike da ni’imomi da albarkatun kasa wadda wadannan albarkatu sun isa su wadatar da kasar da al’ummar ta, ta yadda za ta shige gaban sauran kasashen Afrika wajen tabbatar da samun kaiwa ga muradun ci gaban da ake hankoron nahiyar Afrika za ta iya kai wa nan gaba.

“Majalisar Dinkin Duniya za ta ci gaba da mara wa Najeriya baya domin kara tabbatar da dorewar ingantacciyar dimokradiyya a cikin yanayi na kwanciyar hankula da dawwamammen zaman lafiya a dunkule cikin tafiya ta mutunta juna tsakanin ilahirin kabilun da ke cikin kasar.” Inji Kallon.

Share.

game da Author