Matsalolin rashin jami’an kiwon lafiya da sauran matsalolin da suka hada da: rashin kayan aiki da tsaftatattun dakuna bugu da kari da matsalar wutar lantarki, sun hadu sun zama alakakai da cikas wajen samar da ingantaccen kulawa da marasa lafiya a kananan asibitoci musamman a cikin karkara a Najeriya. Wani kwakkwaran bincike da PREMIUM TIMES ta yi ne ya tabbatar da haka.
Gwamnati mai mulki a karkashin jam’iyyar APC, ta wanzar ko a ce ta kaddamar da shirin ta na inganta kiwon lafiya a matakin farko, PHC a fadin kasar nan, domin kamar yadda ta ce: “a samar wa talakawan kasar nan saukin kulawa da kiwon lafiyar su.”
An yi wannan tsarin ne tun da farko, da nufin giggina sabbin kananan asibitocin kula da marasa lafiya a matakin farko, amma a cikin shekarar da ta gabata, sai hakan bai yiwu ba, maimakon giggina sabbi da aka yi alkawari, sai aka ce za a gyara guda 10,000 (dubu goma) da ake da su.
Wannan shiri dai an sa masa suna Shirin Fardado da Kiwon Lafiya a Matakin Farko, a karkashin hukumar kula da lafiya a matakin farko, wato, NPHCDA, wadda ke a karkashin Ma’aikatar Kula da Lafiya ya Kasa.
Shugaba Muhammdu Buhari ne da kan sa ya kaddamar da wannan shiri a ranar 10 Ga Janairu, a lokacin da ya shirin na gyara da ingata kananan asibitocin a Kuchigoro, wani kauye a gefen Abuja. An dai inganta wannan cibiya da jami’an kiwon lafiya, an damfara mata kayan aiki domin kula da dimbin marasa lafiyar da ke zuwa wurin. Sai dai abin takaici, sauran cibiyoyin kula da lafiya da ke sauran wurare a fadin kasar nan, ba kamar yadda ta Kuchigoro su ke ba.
Yayin da PREMIUM TIMES ta kai ziyara a cibiyar da Asata a cikin yankin al’ummar Ogui a jihar Enugu, cibiyar kula da Lafiyar a lalace ta ke, kamar yadda sauran akasarin na sauran jihohi su ka a lalace. Babbar matsalar ma ita ce yadda ake jekala-jekalar karba da kula da marasa lafiya a cibiyoyar.
“Mu fa nan idan za mu karbi mata masu haihuwa, to tunda ba mu da wutar lantarki sai dai mu yi amfani da cocila mu haska mu taya mai nakuda haihuwa.” Haka jami’in kula da lafiya ya shaida wa wakilinmu a Asata, amma kuma ya ce kada a bayyana sunan sa, don kada cibi-ya-zama-kari.
“Ga shi dai wannan cibiyar kula da marasa lafiya karama ce kwarai, amma jama’a da dama sun a zuwa a duba lafiyar su a kowacwe rana. Ka san mutane fa yanzu ba kudi. To jama’a marasa lafiya na cikin gagari sosai. Mu kan mu jami’an kula da lafiya, wasu lokuta wasu ba su da kudin da za su hau mota zuwa nan wurin aiki. Sannan kuma babu wadatattun ma’aikata a cibiyar nan.”
Ya kamata a ce mu na da masu shara da goge-goge, masu gadi da dare, amma duk babu ko daya. Ga shi ka dai gani wannan ginin ya yi kankanta, tagogi da gidan sauro duk sun yage.”
“Mu fa nan mun kai sama da shekara daya mu na fama da matsalar wutar lantarki. Ko sau da yaba a kyallo wuta ba a cikin shekara daya. Sai dai kawai mu rika yin amfani da cocila ko kuma fitilar jikin wayar selula. Akwai janareto, amma ya dade da lalacewa, an ki a gyara shi.”
A cibiyar kula da lafiya ta Kuduru da ke Bwari kuwa, PREMIUM TIMES ta gano cewa rabon su da wutar lantarki bana shekara hudu kenan, tun ma da aka gina cibiyar kenan. Domin an bayyana wa wakilinmu cewa an gina cibiyar cikin watan Mayu, 2011, amma sai cikin 2013 ta fara aiki.
‘‘Babun fa ta yi mana yawa, ba wutar lantarki kuma babu ruwan famfo. Kullum sai mun kira dan-garuwa mun sayi ruwa a wannan asibitin.”
Da aka tambaye su yadda suke aiki tunda babu wutar lanyarki, wani jami’in ya ce idan muka fito 8 na safe, mu na tashi karfe 4 ko 5 na yamma, idan kuma akwai mai nakudar da za ta haihu, kuma ga duhu, sai mu lalubo fitilar da ake cajawa domin ita kadai ce mafita tunda ko janareta ba mu da shi.”
A cibiyar kula da lafiya ta Dutsen Alhaji kuwa, da ke Dutse Makaranta, cikin karamar hukumar Bwari da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja, abin ba dadin ji, kuma babu kyawon gani. A can dai babu matsalar wutar lantarki, amma kazanta ta yi yawa, ginin asibitin ya lalace, kuma da wuyar gaske wanda hanya ta bi da shi zai wuce ya yarda cewa a wurin har jarirai ake haihuwa.
“Kamar dai yadda ake gani, ginin nan dai ya tsufa, bai kamata a ce asibitin kula da lafiya ba ne wannan. Muna samun dimbin marasa lafiya a kokwace rana.” Haka wata jami’a ta shaida wa PREMIUM TIMES.
Shi ma na Idu Karmo da ke karkashin Babban Birnin Tarayya, Abuja, hakan ya ke, ba su ma san da hasken wutar lantarki ba a mafi lokuta, sai dai su ji labari.
Amma wata majiya ta bayyana wa PREMIUM TIMES cewa su da kan su sun yi karo-karo, su ka hada kudi suka samar da lantarki mai amfani da hasken rana, wato sola.
“Idan babu wuta, tunda ba mu da janareta, sai mu yi amfani da hasken sola. Mun daina zaunawa mu na jiran sai gwamnati ta waiwayo mu.” Haka wani ma’aikacin cibiyar ya bayyana.
Jmama’a da dama za su jira su ga abin da kasafin kudi na 2017 zai tanadar wa harkar kiwon lafiya a matakin farko, domin gwamnatin tarayya ta mika har sama da naira bilyan 19 domin kashewa a fannin kiwon lafiya a matakin farko.