Wata yarinya mai shekaru 14, da ake zargin ‘yar Boko Haram ce, ta bayyana cewa shugabannin Boko Haram sun yi mata asiri kuma sun rika dirka mata kwayoyi domin ta kai hare-haren bama-bamai a Maiduguri, saboda ta ki amincewa ta auri daya daga cikin mambobin kungiyar a cikin Dajin Sambisa.
Wacce ake zargin dai ta na daga cikin wasu uku da sojoji suka cafke a yayin da suke kokarin kai harin kunar-bakin–wake kan sojoji a Jakana, Maiduguri.
Ta shaida wa kafar yada labarai ta NAN a Maiduguri cewa an sace ta ne tare da mahaifin ta, mai suna Usman, a Gwoza, cikin 2013.
Ta ce ita da mahaifin ta sun gamu da Boko Haram ne a lokacin da suke gudun tsira a kan tsaunin Mandara, sai suka yi arba da su, aka sace su. Ta ce sun yi niyyar tserewa ne zuwa Madagali ta jihar Adamawa, inda suke sayar da shanu, amma sai suka yi rashin sa’a, Boko Haram suka cafke su.
“Na shafe shekara uku a hannun Boko Haram, inda mambobin su uku kowa ya nemi ya aure ni, amma na ki amincewa. Biyu daga cikin su ma kwamandoji ne.”
Da na ki amincewa ne, har a karo na uku, sai suka harzuka, sai suka ce za su kashe ni su kashe mahaifina. Ni kuma na ce ai gara na mutu da na auri dan Boko Haram.”
“ Bayan haka ne fa suka yi mini allura inda daga nan ban sake sanin komai da ke faruwa da ni ba.
“ Bayan na farfado sai naga kai na a dakin wani Boka inda yace kwanana 30 kenan ina wajensa ya na shirya tsafi akaina da shirya ni akan wani aiki da zan fara yi. Daga nan sai ya bani wani magani na sha sannan kuma yace wadanda suka kawo ni zasu zo yau su tafi da ni.
“ Da karfe bakwai na yamma na yi kuwa sai Boko Haram su ka zo da wani saurayi da wata yarinya.
“ Mun dauki kusan awa daya da rabi muna tafiya kafin mu kai Maiduguri. A daidai muna isa Maiduguri sai naga suna daura mana Kambun bamabamai, daga nan ne sai na fara hawaye domin nasan shike nan mutuwa ta tazo.
“ Ina kallon yadda mace ta farko da muka zo tare da ita ta tada bam din dake jikinta kusa da wurin da Sojoji ke duba mutane. Amma bai kashe kowa ba sai ita da take dauke da bam din.
“ Na biyu kuwa kafin ya tada bam din sojojin sun harbe ta.
“Ina ganin haka sai na cire nawa na yar kafin sojojin suyi harbi sai na fadi kasa sume.
“ Ni dai na farfado ne naga kaina a wajen wasu ‘yan sanda inda daya daga cikinsu ma Kanin Mahaifiya ta ce. Ina ganin dalilin da ya sa ba’a kashe ni ba Kenan.