Wani magidanci ya lakadawa mahaifin matarsa dukan tsiya, ya sari mahaifiyarta da adda a Kano

1

Wani magidanci a garin Garimallam dake jihar Kano mai suna Danladi Jobawa ya lakada wa iyayen matarsa shegen duka saboda fusata da yayi da har yanzu ba a san ko menene sanadiyyar hakan ba.

Da yake amsa tambayoyi a garin Kura, Danladi ya shaida wa Dantala Kura cewa Tsautsayi ne ya same shi amma shima kansa bai san menene ya kaishi ga yin haka ba.

“ Tsautasyine ya debe ni cikin dare da misalign karfe daya da rabi na dare na tafi gidan iyayen matana nayi sallam.

Da suka tambayeni dalilin zuwa gidan cikin wannan dare sai nace musu, yar su ce bata da lafiya sai ko mahaifinta ya bude , bayan ya bude kofar sai na haushi da sara inda ita ma sirikar tawa da ta fito bayan ta ji ihun mijinta sai na hada da ita na hau duka da sara.

Jin ihun su da sallallami da makwbta da suka ji shine suka fito sukayi tarar tara sanna aka kama Danladi suka mika shi ga hukuma.

Danladi ya tabbatar wa jami’an tsaro cewa bashi da tabin hankali kuma shi ba mashayi bane.

“ Ni dai wannan abu tsautsayine kuma dai ina ganin Azal ce kawai ta fado mini.”

Yanzu dai a halin da ake ciki Danladi na tsare a gidan yari domin sirikan nasa sun shigar da kara kotun musulunci da ke Kura sannan kuma haryanzu ana ci gaba da sauraron karan.

Ita maidakin Danladi ta koma ga iyayen ta domin tace ba za ta iya zama da mijin nata ba.

Mahaifin matar Danladi na kwance haryanzu a asibiti ya na karbar magani a dalilin illatashi da Danladi yayi a harin da ya kai masa.

Sannan kuma Danladi na ta neman gafarar iyayen matarsa kan abin da ya aikata musu cewa su yafe masa.

Ana sa ran dai cewa azaman koto na gobe kila a saki Danladi bayan nadamar da yayi akan abin da ya aikata da neman ayi sulhu da yakeyi.

Share.

game da Author