Tun muna yara ‘yan kanana mun san ana cutar sankarau. A wancan lokacin mun san ita wannan cuta ta sankarau, ba a lokacin damina ko sanyi ake samunta ba, tana zuwa ne a lokacin da ake tsananin zafi.
Haka kuma mun sani a bisa al’ada har zuwa yau yara kanana a wannan nahiya tamu ba a yi musu kaciya sai a lokacin sanyi. Malaman kimiyya na gargarjiya, wato wanzamai, su sun haqqaqe kaciya ta fi saurin warkewa idan an yi ta a lokacin sanyi.
Har wala yau, cutar kurkunu, wanda na daina jin labarinta kwata-kwata tafi yaduwa da yawa a lokacin damina. Sauro ma yafi kara-kaina a lokacin zafi da damina, cutar da yake yaxawa ta maleriya ta fi kamari a zafi da damina.
Duk wadannan batutuwa ilmi ne,kuma tabbatacce, babu wanda yake ja da wannan batu a tsawon lokaci. Ilmi ne wanda kunne ya girmi kaka.
Masu bin kafafen labarai sun ji cewa zuwa jiya Litinin ministan harkokin lafiya na kasa Farfesa Onyebuchi Ezekeil, ya bada bayani cewa an samu vullar cutar sankarau a jihohi 19 na Najeriya, a sakamakon vullar cutar har an rasa rayuka sama da 400, sannan ga mutum dubu hudu suna cikin halin damuwa mai ban tsoro a duk fadin kasar dangane da wannan cuta ta sankarau. Ya fadi wannan bayani ne a Gusau, jihar Zamfara inda akalla yara 230 suka rasa rayukansu sakamakon wannan musiba.
A yau kuma a jihar Kaduna, ministan ya yi bayanin cewa gwamnati ba ta da wani shiri akan wannan sabuwar Sanqarau TYPE C, ita shirin da take da shi shi ne akan abin da aka saba gani na cutar da ake yi wa laqabi da Sanqarau TYPE A.
Abin da ya fi daukar hankali tun bayan bullar wannan annoba da suka saba ji da gani shi ne sabuwar fassarar abin da ya jawo cutar.Tun fil azal, masana sun nuna zafi da cunkoso da rashin iska sune suke qarawa wannan zazzabi kwarin gwiwa idan kwayar sa ta bakateriya ta fara yaduwa. Da wahala kuma a danginku a ce an rasa wanda wannan cuta ta tava kashewa a shekaru 100 da suka gabata tun lokacin da aka fara jin duriyarta.
Ma’aikatar lafiya ta qasa da haxin gwiwar takwarorinta na jihohi sukan yi tanadi akanta idan zafi ya fara nuna alamun shiga.Musamman kuma a bana, masana sun bada gargadi cewa za a samu sanqarau mai muni kuma TYPE C, don haka a yi maza-maza a xauki matakan rigakafi.
Amma kuma kwatsam sai ga gwamnan jihar Zamfara yana shaida wa duniya cewa wannan cuta ta sankarau abin da ya kawo ta ba abin da mutane suka saba ji bane ko wanda suka sani na asali, wannan karon sabon Allah ne da ya yi yawa, musamman kuma zinace-zinace shi ne dalilin da ya sanya Allah ya kawo cutar da tafi kowa qarfi ta faskari duk wani magani ta ke kashe mutane cikin qiftawa da bisimilla.
A fahimtar Alhaji Abdul Aziz Yari, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar gwamnoni ta qasa wato Nigerian Governors Forum mutane su koma ga Allah su gyara tsakaninsu da shi, sai a warware daga wannan tashin hankali da musiba.
Ba shakka Allah SWT yana jarrabtar bayinsa da musibu iri-iri domin su hankalta sannan kuma su koma gare shi.
Amma irina za su gamsu da fahimtar Abdulaziz Yari ne kawai idan da gwamnatinsa ta jihar Zamfara ta yi tanadi bisa shawarwarin masana domin dakile wannan musibar da an gaya musu tana zuwa.Sun yi bakin kokarinsu, sai ta gallabesu, sai mu ce eh yana da hujja. Amma ya zauna yana ta yawo, yana sharholiyarsa, bai zama a Gusau, bai zama a Talatar Mafara, cuta ta vulla, kawai sai a ce Allah ne? Allah ai baa bin wasa bane! Ai ita musibar da Allah ya ke aikowa tana zuwa ne ga muatne ba shiri wato bagatatan. Amma Sankarau ai an san shi da gidansu, da unguwarsa da iyayensa, kuma an saba da shi, har na bana wannan sabon akwai labarin zai zo.
Zan kuma iya yarda da matsayin AbdulAziz Yari da a ce wadanda cutar ta ke kashewa ba yara bane. Akasarin mutanen jihar Zamfara 230 da suka rasa rayukansu a wannan annoba, ‘yan yara ne qanana da suke qasa da shekara goma. Masu wannan shekaru a shari’ar Musulunci basa xaukar laifi kama Allah ba zai kama su ba, suna can makarantar Annabi Ibrahim AS. Idan muka yarda da matsayin gwamna Yari, mun gamsu kenan Allah (SWT) mai sabawa ne ciki maganganunsa kuma yana hukunta wanda laifi bai shafe shi ba. Ba kuwa haka bane.
A hankalce kuma in aka dogara ga fahimtar AbdulAziz Yari, duk wani magani da za a nema daga WHO ko UNICEF ko qasashen Turai da Larabawa da Asiya bai dace ba, tunda cutar ta fi qarfin tunanin xan adam, zura ido za a yi a ci gaba da addu’a kuma ana yakar alfashar zina, sai Allah ya kawo sauqi. Wannan kuwa mustahilli ne.
A zance na gaskiya abubuwa biyu ne ko uku za a yi domin shawo kan wannan matsala a yau da guje mata a gobe. Na farko mu daga hannu mu roki Allah mu nemi taimakonsa domin ya kawo mana sauqi da rangwame a cikin irin wannan halin da muka shiga na wannan annoba. Na biyu kuma mu fita neman magani a ko ina yake a duniya domin tseratar da rayuwar al’ummarmu, yana daga cikin alqawura da rantsuwa da shugabanni suke karva idan sun hau mulki na tsare dukiya da rai da lafiya.Wajibi ne gwamnoni da shugaban qasa da duk masu alhaki a cikin wannan sha’ani su bi duk wata hanya da duk wata dabara domin a kau da ita. Rai fa na mutum xaya ba abin wasa ba ne. Na karshe kuma shi ne , duk abin da yake rataye a wuyan gwamnati, kuma ta san alhakinta ne, ya zama tilas ta riqa daukar mataki a kan lokaci tun kafin ya zo ya gagara warwarewa. Sankarau din nan an san shi kuma ana da labarin cewa yana nan tafe da sabon salo mai muni, ba daidai bane a yi sakaci, sai ya zo kuma a dorawa Allah mahalicci laifi, har ma a yi masa karya.
Irin wannan fahimta da Yari yake son mutane su hau kanta su zauna, ba zata taimaka mana ba a samu shawo kan wannan mas’ala ta didindin. Ai wasu kasashe da yawa a duniyarmu ta yau inda suke da zafi sun yi bankwana da cutar Sankarau, kai idan muka yi la’akari da tarihin Sanjarau a Najeriya, za mu ga cewa akasarin jihohin da abin ya fi shafa suna yankin Arewa, ko a wannan zafin jihohin kudu hudu ne abin ya shafa, sauran 15 a Arewa ne. Ka ga za a iya maganinta in an ga dama.
Za a iya samun Bello Muhammad Sharada a:bellosharada@gmail.com