Daya daga cikin kyakkyawan tunanin da Tshohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya yi, shi ne kafa Hukumar Yaki Da Almundana Da Zambar Kudade, wato EFCC, wacce a farkon kafa hukumar, sai aka nada babban jami’in dan sanda, Malam Nuhu Ribadu domin ya shugabance ta.
EFCC ta yi jan aiki a lokacin, duk da dai a gefe daya an rika zargin ta da cewa ana amfani da Hukumar ana musguna wa wadanda ba su shan inuwa daya da Obasanjo.
Kadan daga cikin nasarorin sun hada da kame Tsohon Sufeto Janar na ‘Yan sanda Marigayi Tafa Balogun. sai kuma James Ibori wanda a karshe bayan ya gudu zuwa Ingila, inda a can suka cafke shi har ya yi zaman bursuna a kasar.
An kuma kama Bode George da Aminu Dabo wadanda dukkan su sai da suka yi zaman kurkuku. Bayan su kuma an sha kama yawancin gwamnonin da suka sauka ana maka su kotuna daban daban.
Sai dai kuma tun da farko babbar matsalar da EFCC ke fama da ita, ita ce jan-kafa da tafiyar hawainiyar da ake yi wa wadannan shari’u na ‘yan siyasar a kotuna.
Har yau akwai kwantan shari’un da ba a kammala ba su na nan a kotu damfare ba a ma san ranar kammalawa ba. Da yawa daga cikin gwamnonin da aka kak-kama a lokacin Ribadu da wacce ta gaje shi, Farida Waziri, sun shiga sabon zabe sun zama ministoci.
A cikin irin wadannan akwai irin su Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki, Sanata Danjuma Goje, Sanata Saminu Turaki da sauran su da yawa.
Dalillan da kan jawo haka, ba su rasa nasaba da yadda wadanda ake tuhumar da wawure kudaden kan dauki kwararrun lauyoyi su na biyan su makes an kudade domin su kare su a kotu. Hakan kan janyo a yi ta wala-wala da shari’un a kotuna, shari’ar da ba ta wuce a kammala a cikin wata uku ba, sai a yi ta jan ta kamar zaren-kurkunu, har sama da shekara bakwai.
Na taba yin hira da tsohuwar shugabar EFCC, Farida Waziri, inda ta shaida min cewa matsalar lauyoyi na kawo wa EFCC cikas. “Su dai wadanda mu ke kamawa da ya ke kudin banza su ke ganin sun tara ba na hakkin gumin jikin su ba, to ba su damu da kashe ko milyan nawa ne ba wajen dauka kwararrun lauyoyi.”
Farida ta kara da cewa gwamnati kuwa ba ta iya kashe makudan kudade wajen daukar manyan lauyoyin. Baya ga wannan matsalar, akwai matsala ta rashin yin kwakkwaran bincike a bangaren jami’an EFCC. Wannan kuwa ba wai ra’ayin Farida Waziri ba ne.
Sau da yawa EFCC na yin gaggawar maka wanda suke tuhuma a kotu. Sai tafiya ta fara nisa, sai kuma su gano wani abu, ko kuma idan an kusa kayar da su a kotu, su nemi a sake kara musu lokacin sake ko kara wasu tuhume-tuhumen da ake wa mai laifi.
Idan wadannan matsalolin sun addabi wa’adin da kowane shugaba ya yi ya na jagorantar EFCC, kama daga Ribadu, Farida, Lamurde da shi kan sa na yanzu Ibrahim Magu.
Sau da yawa za mu ga ga barawo an kama da kaya a bisa kan sa, amma saboda rashin kakkwarar shaidar kudin na sata ne, tilas kotu ta sallami wanda ake tuhuma.
Babban misali a nan shi ne shari’ar kwanan nan wacce kotu ta wanke wani babban mai shari’a, wanda aka kama da naira milyan dari biyar. Wata matsala kuma ita ce irin yanayin da ake bi ana kamo wadanda ake tuhuma.
Misali shi ne irin kamun da jam’in DSS su ka yi wa alkalan da aka yi zargi sun karbi toshiyar baki a zaben 2015. Me ya sa DSS za su rufe idanu a lokacin da suka kai masu samame? Ka na babban alkali, karti sun shigo gidan ka tsakar dare sun rufe fuskokin su, sun kwantar da kai kasa, sun hau kan benen gidan ka sun fito da makudan kudade sun ce ga abin da suka gani, son haka ka sa hannu cewa naka ne. Shin wa zai iya kin sa hannu a lokacin?
Wannan zai ba mutum damar idan an je kotu ya ce kudi ba na sa ba ne, shigowa aka da su domin a kula masa sharri.
Irin yadda ake wa aikin EFCC fassara ta siyasa, shi ma abin damuwa ne matuka, kuma ya na rage wa hukumar karfin goyon bayan da ta ke samu. Akwai masu yi wa wadanda su ka saci dukiyar gwamnati ikirarin cewa sun ci bilis. Wani kallon jarumi ko wani gwarzo. Ba a dade da sakol tsohon gwamnan Delta, James Ibori daga kurkukun Ingila ba, amma dawowar sa Nijeriya har an ba shi sarautar gargajiya.
Akwai kuma masu kallon cewa wasu na cikin gwamnati mai ci, sannan masu kashi a gindi na kawo wa yaki da rashawa kafar-ungulu. Dama kuma ‘yan hadawa na cewa gwamnatin APC cike ta ke da tulin wadanda suka taimaka aka kassara kasar nan tsakanin 2010 zuwa 2015, amma an kyale su.
Babban misali shi ne yadda EFCC ta bayyana cewa ta na farautar tsohon gwamnan Jihar Saminu Turaki ruwa a kallo. Bayan sanarwar an ga Saminu a Daura ya je daurin auren ‘yar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, kuma an gan shi a wani taron ba da dadewa ba.
Kafin nan kuma, sau da yawa ba a ganin mai gabatar da kara na EFCC ko Saminu ko lauyoyin sa a ranar shari’ar a kotu.
Ya kamata EFCC ta kama hanyar kara bai wa jami’an ta horo da kuma sake daukar kwararru. Ta rika yin kyakkyawan bincike kuma a rika daukar manyan lauyoyi. Hakan zai gaggauta saurin yanke hukunci ga wadanda ake tuhuma.
Shin idan za mu tambayi juna, daga cikin wadanda aka kame a shekaru biyun nan, mutum nawa ke kurkuku? Ga shi kuma sai kara bankado bilyoyin kudaden da aka wawura ake yi, amma kotu ba ta daurewa. Jama’a mu duba mu gani. Ko kuwa dama can Buhari ne kadai ya damu kakkabe dattin rashawa, cin-hanci, almundahana da zambar kudade a Nijeriya?
Ashafa Murnai, Mataimakin Edita ne a gidan jaridar PREMIUM TIMES Hausa.
Imel:mashafa96@yahoo.com