Buhari ya nada Abdulhamid Dembos babban Darekta a gidan Talabijin na kasa

0

Tsohon shugaban gidan Talabijin na kasa ta Kaduna NTA Abdulhamid Dembos ya zama sabon babban darekta mai kula da harkar kasuwanci a gidan Talabijin na kasa.

Dembos ya rike mukamin shugabancin kungiyar ma’aikatan gidajen Talabijin da Rediyo na kasa wato RATTAWU, sannan kuma ya zamo shugaban gidan Talabijin na NTA dake jihar Kogi da na Kano kafin ya dawo Kaduna a matsayin shugaban na shiya.

Bayan haka kuma jagoran shirin nan maisuna Hannu da yawa a gidan Rediyon tarayya na Kaduna Buhari Auwalu ya dare kujeran shugaban gidan Rediyon.

An nada Aliyu a matsayin shugaban kwamitin gudanarwan gidan Rediyon.

Mustapha Yunusa Maihaja kuma ya canji Sani Sidi a hukumar NEMA.

Share.

game da Author