Wani jigo a kungiyar Boko Haram ya mika wuya

0

Wani jigo dan kungiyar Boko Haram mai suna Bulama Kailani Mohammed Metele ya mika kansa ga Jami’an sojin Najeriya a Damasak.

Bulama ya na daga cikin jerin wadanda aka saka hotunansu da gwamnati ke farauta ruwa a jallo.

kakakin rundunar sojin Najeriya Birgediya Janar Sani Kukasheka Usman ne ya sanar da wannan nasara da aka samu.

Ya ce Bulama dan bangaren Boko Haram din Muhammed Nur ne kuma a tuhumar sa yanzu haka.

Kukasheka ya ce an kama wadansu ‘yan Boko Haram guda biyu a kauyukan Kareto da Dangalti dake jihar Barno din a lokacin da suke kokarin nemo bayanai akan kauyukan domin far musu.

Share.

game da Author