Gidan Rediyon Tarayya na Kaduna, Hukumar NEMA, NTA sun sami sababbin shugabanni

0

Shuagaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin sababbin darektocin wasu ma’aikatun gwamnati da shugabannin kwamitin gudarwan ma’aikatun.

Wadanda aka nada sun hada da Duro Onabule wanda zai shugabanci kwamitin gudanarwan gidan talabijin na kasa wato NTA.

Sauran darektocin sun hada da Steve Egbo, Abdul Hamid Salihu Dembos, Mohammed Labbo, Fatima M. Barda, Stephen Okoanachi da Wole Coker.

Bayan haka an nada Mustapha Yunusa Maihaja sabon shugaban hukumar bada agaji na gaggawa wato NEMA, Mustapha ya canji Sani Sidi wanda shine shugaban ta kafin wannan sabon nadin.

Buhari Auwalu ya zamo sabon shugaban gidan rediyon tarayya na Kaduna inda aka nada Yinka Amosun babban darektan gidan rediyon tarayya dake jihar Legas.

Share.

game da Author