Gwamnan Kaduna Uba Sani ya kaddamar da raba abincin tallafi na biliyoyin Naira ga talakawan Kaduna.
A jawabinsa a wurin taron kaddamarwar ranar Litinin a Kaduna, gwamna Sani ya bayyana cewa gwamnati za ta raba wa akalla talakawa miliyan daya abinci da suka hada da shinkafa da masara
” Gwamnati za ta raba wa marasa karfi da talakawa abincin tallafi ne domin rage radadin da mutane ke fama da shi na rashin abinci. Za a raba manyan motoci cike makil da shinkafa da masara 128 da kudinsu yakai naira Biliyan 3.4.
” Za a raba wa gidaje akalla 200,000 a fadin jihar wanda ya yi daidai da akalla mutum miliyan 1 kenan za su amfana da wannan tallafin. Tuni har motocin abincin sun kama hanyar zuwa kananan hukumomi.
Gwamna Sani ya ce za a raba tallafi ga kananan masu sana’a na naira biliyan 4 a fadin jihar.
Discussion about this post