A cikin daren Lahadi ne ‘yan ta’adda suka far wa kauyen Senta two dake karamar hukumar Kajuru suka arce da mutane sama da 100.
Wannan hari ya auku ne mako guda da sace wasu mutum 71 da aka yi a Buda, duk a karamar hukumar.
Wani mazaunin garin da ya tattauna da PREMIUM TIMES ya shaida cewa maharan sun shigo garin da misalin karfe 10:30 na daren Lahadi ne inda suka rika shiga gida-gida suna kwashe mutane.
Wasu ma sun fara bacci, wasu ko riga basu da shi a jiki.
Sai dai kuma ranar Litinin da misalin karfe 4 na yamma sai suka sako mutum bakwai, 3 mata 3 maza da mace daya mai shayarwa.
Sai dai kuma haryanzu jami’an tsaron da kwamishinan tsaron jihar Kaduna Samuel Aruwan ba su ce komai akai ba.
Discussion about this post