Rundunar ‘yan sandan jihar Akwa-Ibom ta bayyana cewa ta kama batagari da a ciki akwai wata mata da ta hada baki da wasu maza hudu suyi a yi garkuwa da ita.
Kwamishinan ‘yan sanda Waheed Ayilara wanda ya sanar da haka ya ce batagarin da suka kama sun kai mutum 52 sannan sun kama su bisa laifin fashi da makami, aiyukan kungiyar asiri, damfara da safarar yara kanana.
Ayilara ya ce matan da suka kama ‘yar asalin kauyen Nung Oku ne dake karamar hukumar Ibesikpo Asutan a jihar.
Ya ce dakarun sun kama ta bisa laifin hada baki da saurayin ta domin yin garkuwa da ita inda har ta bukaci kudin fansa naira miliyan hudu.
Yan sanda sun samu labarin garkuwar ne bayan wani Enobong Sampson ya sanar da jami’an tsaron cewa masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da ‘yar uwansa kuma sun bukaci naira miliyan hudu kudin fansa.
“Nan da nan jami’an mu suka fara gudanar da bincike tare da tattaro bayanan sirri domin kamo mutanen.
“A ranar Talata dakarun suka kama matan tare da saurayinta a maboyar su dake Mbierebe Obio dake karamar hukumar Ibesikpo Asutan.
“Bayan sun shiga hannun jami’an tsaro matar ta tabbatar cewa ta hada baki da saurayin ta da wasu maza uku domin a yi garkuwa da ita.
“Matar ta ce ta yi haka ne domin ta samu kudi daga hannun goggonta dake zama a kasar waje.
Discussion about this post