Gwamnatin jihar Gombe ta bayyana cewa mutum 95 sun kamu da cutar Sankarau yayain da cutar ta yi ajalin mutum shida a jihar.
Kwamishinan lafiya na jihar Habu Dahiru ya sanar da haka ya ce mutum shida din da cutar ta yi ajalinsu an same su a kananan hukumomi biyu a jihar.
“Mutum biyar sun mutu a kananan hukumomin Nafada da Funakeye.
Dahiru ya ce cutar ta fara bayyana a karamar hukumar Nafada ranar 18 ga Faburairu inda aka samu wasu da alamun cutar.
Ya ce zuwa yanzu mutum 83 daga cikin mutum 95 din da suka kamu da cutar an sallame su daga asibiti.
Dahiru ya ce gwamnati tare da hadin gwiwar WHO, NCDC da UNICEF za su fara wayar da kan mutane game da cutar ta hanyoyin samun kariya daga kamuwa da ita.
Ya kuma ce jami’an lafiya za su mai da hankalin su wajen ganin sun dakile yaduwar cutar musamman a kananan hukumomin da cutar ta bayyana.
Cutar Sankarau
Sankarau cuta ce da kwayoyin suka hada da ‘Bacteria, Virus da Parasite’ ke haddasa cutar a jikin mutum.
Mutane musamman yara kanana na yawan kamuwa da cutar a duk lokacin da yanayi ya canza zuwa lokacin zafi.
Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa NCDC ta bayyana cewa daga shekarar 2022 zuwa 2023 mutum 303 sun kamu da cutar sannan cutar ta yi ajalin mutum 190 a jihohi 29 da Babban Birnin Tarayya Abuja.
NCDC ta kuma ce duk jihohi 19 dake yankin Arewacin Najeriya da jihohin Bayelsa, Cross River, Delta, Ekiti, Ogun, Ondo da Osun dake kudancin kasar nan na daga cikin bangarorin kasar da suka fi yawan fama da bullowar cutar.
Bana dai Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya NiMet ta yi hasashen cewa bana jihohin Sokoto, Jigawa, Yobe da Borno na daga cikin jihohin da ka iya samun barkewar cutar saboda canjin yanayi na zafi da za su rika samu.
Alamun kamuwa da Sankarau
1 Za ka ga yaro yana ta suma idan ya kamu da cutar.
2. Yawan kwanciya da gajiya
3. Yawan yin Amai
4. Cutar na kawo amai.
5. Curar na kawo zafin jiki wanda daga baya yakan iya zama Zazzabi.
6. Mutum zai dinga ganin jiri
7. Sankarewan wuya.
8. Rashin son ganin haske.
Hanyoyin gujewa kamuwa da Sankarau
1. Yin allurar rigakafi.
2. Tsaftace muhalli.
3. Rage cinkoso a wuri daya.
4. Abude tagogi domin samun isasshen iska a dakunan da ake zama.
5. A daina ganin cutar Sankarau a matsayin wani tsafi ne ko jifa.
Discussion about this post