Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani a ranar Litinin ya kaddamar da kwamitin mutum 10 don sake tsugunar da al’ummar Kudancin Kaduna da suka rasa matsugunansu sakamakon rikicin da aka kwashe tsawon shekaru ana yi a yankin.
PUNCH ta buga cewa Kungiyar al’ummar Kudancin Kaduna ta yaba da matakin, inda ta bayyana matakin a matsayin abin a yaba da farinciki ga mutanen yankin.
Yunkurin sake tsugunar da matsugunan ya biyo bayan shawarar da kwamitin tsaro na jihar ya bayar a ranar 8 ga watan Nuwamba, 2023, na cewa akwai bukatar gwamnatin jihar ta kafa kwamitin da zai sake tsugunar da al’ummomin da suka rasa matsugunansu.
Kwamitin mai mutum 10 yana karkashin jagorancin mataimakiyar gwamna Dr. Hadiza Balarabe tare da sakataren gwamnatin jihar, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, da shugabannin kananan hukumomin Jema’a, Kaura, da kuma karamar hukumar Zangon Kataf.
Yayin kaddamar da kwamitin a gidan gwamnati da ke Kaduna a ranar Litinin mataimakiyar gwamnan, wacce ta wakilci gwamnan, ta jaddada cewa gwamnati na bukatar a hada hannu don tabbatar an tsugunar da al’ummomin da suka rasa matsugunansu.
Gwamna Sani ya ce halin da ‘yan gudun hijirar ke ciki na ci wa gwamnatin jihar tuwo a kwarya, don haka akwai bukatar daukar kwakkwaran mataki don biya musu bukatunsu da kuma samar musu da matsugunnai.
Gwamnan ya bukaci kwamitin da ya tunkari aikin cikin tausayawa, adalci, da kuma cikin gaggawa.
Discussion about this post