Da farko dai Gwamnatin Tarayya ce ta fara tallafawa da Naira biliyan 90, yayin da ta ga kuɗin tafiya aikin Hajji ya tashi daga Naira miliyan 4.9 ya kai Naira miliyan 8 da ɗoriya, bayan tashin Dalar Amurka.
Tallafin Naira biliyan 90 da Gwamnatin Tarayya ta bayar ne ya maida kuɗin tafiyar ya koma Naira miliyan 6.5.
Hakan ya na nufin kowane maniyyaci zai cika Naira miliyan 1.9 kenan. Amma da gwamnatin tarayya ba ta bada Naira biliyan 90 ba, to kowane maniyyaci sai ya cika Naira miliyan 3.5 kenan.
Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta ce cikon naira biliyan 230 ta nema a wajen gwamnatin tarayya, amma sai ta samu Naira biliyan 90. Hukumar ta ce da gwamnatin tarayya ta biya Naira biliyan 230, to ba za a umarci kowane maniyyaci ya cika ko sisi ba.
An dai rufe karɓar cikin kuɗaɗen a ranar Juma’a, 29 ga Maris, ƙarfe 12 na dare.
Yayin da wasu maniyyatan suka karɓi kuɗaɗen da suka biya, wasu jihohin kuma sun tallafa wa maniyyatan, kamar Kano, Kogi, Osun da Bauchi.
Kano ta ba kowane maniyyacin jihar gudummawar Naira 500,000. Baki ɗaya Kano ta bayar da Naira biliyan 1.4. Jihar Osun ma ta bayar da haka Jihar Kogi ta cika wa baki ɗayan su 460 Naira miliyan 800.
Jihar Bauchi ta bai wa kowane maniyyaci cikon Naira 959,000, wato kashi 50 bisa 100 na ƙarin kuɗin da aka yi. Maniyyatan Bauchi su 2,290.
Baki ɗaya Bauchi ta taimaka da Naira biliyan 2.19.
Discussion about this post