Wani masanin abinci mazaunin garin Kaduna Malam Lawal Bala ya bayyana cewa shan faten tsaki na a lokacin sahur na sa kada mutum ya ji azumi wannan rana.
Da yake tattaunawa da PREMIUM TIMES HAUSA a garin Kaduna, ranar Alhamis, Bala ya ce abincin da ya fi dacewa a rika ci a lokacin sahur domin a samu raguwar raɗaɗin yunwa da rana lokacin azumi.
” Wato fate na da matuƙar tasiri a ciki. Ya kan dade hanji bai markaɗeshi shi ba saboda irin sanadarorin da ake haɗawa a lokacin da ake yin shi.
Dubi da irin haɗin da ake masa lokacin hada shi, Alaiyaho, albasa mi lawashi, tsaki ko kuskus, kayan miya da sauran su.
Gambo ya kara da cewa ” mun yi gwaji da masu azumi biyu, daya ya yi sahur da tuwo dayan kuma faten tsaki, amma kafin la’asar wanda ya narki tuwo ya yi la’asar, shi ko wanda ya sha fate, na tsaye ƙem, har sai da aka sha ruwa. Babu alamar wahala a jikin sa.
Sai dai kuma PREMIUM TIMES ba ta iya tantance wannan bincike na Muda ba ta hanyar kimiya domin tabbatar da sahihancin sa.
Wasu da suka zanta da jaridar sun ce, tuwo ne maganin azumi a garinsu. Wasu ma cewa suka yi gurasa da shayi suke sha, kuma daram.
Discussion about this post