Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya gana da jiga-jigan mambobin masu masana’antu da kuma wasu gwamnonin jihohi dangane da mawuyacin halin da tattalin arzikin Najeriya ya afka, gami da irin raɗaɗin tsadar rayuwar da ake fama da shi a faɗin ƙasar nan.
A ganawar wadda wasu gwamnoni suka halarta, sun tattauna matsalar yadda darajar Naira ta zube ƙasa warwas, ita kuma Dalar Amurka sai ƙara yin sama ta ke yi.
Daga cikin waɗanda suka halarci taron a ɓangaren hamshaƙan masu masana’antu da manyan kamfanonin zuba jari, akwai:
Aliko Ɗangote, Abdulsamad Rabi’u mai BUA, Tony Elumelu mai Bankin UBA, Segun Ajayi-Kadir, Babban Daraktan Ƙungiyar Masu Masana’antu ta Najeriya (MAN).
A ɓangaren gwamnoni kuma akwai na Ogun Dapo Abiodun, na Anambra, Charles Soludo a taron wanda aka yi a Fadar Shugaban Ƙasa, a ranar Lahadi.
Tinubu ya shaida wa hamshaƙan cewa an shirya taron ne a dubi abin da gwamnati ke yi wanda shi ne daidai, sannan kuma a duba hanyoyin da za a bi domin a farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa.
Tinubu ya ce yayin da gwamnatin ba ta da dukkan laƙani da fahamin da za ta magance dukkan matsalolin, duk da haka za ta ci gaba da lalube, “har sai ta samar wa ƙasar nan nagartaccen tsari da fasalin tattalin arziki wanda zai ɗora ta kan hanya madaidaiciya.”
“Kamar yadda na faɗi, nauyin da ke kan mu kawai shi ne mu daɗaɗa wa ‘yan Najeriya, ba ‘yan wata ƙasa ba. To kuma mun damu sosai dangane da halin da kowa ke ciki, tun daga ɗalibai, iyaye mata da iyaye maza, manoma, ‘yan kasuwa, ‘yan tireda. Mun fahimci dukkan mu dai duk daga cikin rijiya ɗaya mu ke shan ruwa,” inji Tinubu.
“Muna ta laluben wasu hanyoyin da zamu bi domin taimakon talakawa da marasa galihu domin mu farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa.”
Jawabin Ɗangote, Rabi’u Da Elumelu:
Bayan fitowa daga taron, Ɗangote, Abdulsamad da Elumelu sun yi wa manema labarai ƙarin haske.
“Ina ganin mun yi ganawa mai amfani sosai, kuma wadda za ta yi tasiri matuƙa. Kuma abubuwan da muka tattauna duk sun dangane matsalar tattalin arzikin ƙasa, matsalar abinci, sai kuma matsalar tsaro da suka addabi ƙasar nan a yanzu. Kuma mun tattauna kowace matsala dalla-dalla,” cewar Ɗangote.
“To akwai Kwamitin Mashawartan Shugaban Ƙasa Kan Tattalin Arziki, wanda Shugaban Ƙasa ya kafa. To wannan kwamiti ne zai duba dukkan batutuwan da muka tattauna domin magance su.
“Kama tun daga samar wa mutane aiki, magance matsalar tsadar abinci da sauran batutuwan da suka shafi tattalin arzikin ƙasa.”
“To duk mun tattauna waɗannan batutuwan dalla-dalla. Ba zan iya ba ku bayanin dukkan abubuwan da muka tattauna ba a yanzu, amma dai muka kyautata zato tare da yaƙinin cewa muna da ƙasaitacciyar ƙasa. Muna da dukkan abin da muke buƙata domin farfaɗo da tattalin arzikin mu, kuma za mu yi haka ɗin.”
A na sa ƙarin bayanin, Abdulsamad Rabi’u ya ce faɗuwar darajar Naira ba ƙayyadajjen abu ba ne. Ya jinjina wa Babban Bankin Najeriya (CBN), dangane da ƙoƙarin da ya ke yi wajen saisaita matsalar.
“Mun tattauna yadda za mu rage tsadar canjin Naira da kuɗaɗen waje. Saboda abin da ke faruwa dangane da canji, ƙirƙirarre ne. Amma mun gode Allah Babban Bankin Najeriya, CBN ya na bakin ƙoƙarin sa matuƙa,” inji shi.
“Yanzu dai Dala ta ɗan sauko daga N1,800 zuwa har N1,500. To kuma kun san dai komai na ƙasar nan sai da kuɗaɗen waje, in dai ana maganar kayan da ake shigo da su ne cikin ƙasar nan.”
Shi kuwa Tony Elumelu, ya ce ya yi amanna idan aka yi amfani da shawarwarin da suka tattauna a wurin ganawar ta su da Shugaba Tinubu, to “za a zaburar da tattalin arzikin ƙasa kuma a sauƙaƙa wa talakawa da sauran jama’a raɗaɗin tsadar rayuwa a faɗin ƙasar nan.”
Ya ce idan aka yi hakan, jama’a za su samu aikin yi ta yadda za su riƙa samun kuɗaɗen sayen abinci.”
Discussion about this post