A daidai lokacin da duniya ta shagaltu kuma take shakatawa da kallon gagarumar wasan super bowl a kasar Amurka, kasar Israila ta dukufa wajen kisan kiyashi kan musulmai da kuma kiristoci mazauna birnin Rafah da kuma sansanin yan gudun hijira dake zirin Gaza.
Jim kadan da fara wannan aika aikar sama da mutane 100 suka rasa rayuwarsu a cikin awanni kadan.
Kasar ta Israila tasha alwashin ci gaba da wannan aika aikan, tare Kuma da yin kunnen uwar shegu da kiran tsagaida wuta da kuma wofantarda kiraye kirayen kawo karshen kisan kiyashi a zirin Gaza. Duniya gaba daya na alawadai da wannan tabargaza face manyan kawayen Israila guda biyu wato Amurka da Ingila.
Kawo yanzu Kasar Yahudawan ta kashe akalla Falasdinawa farar hula 35,000 a cikin makwanni hudu daga cikinsu sama da 17,000 kananan yara, haka kuma an jikkata sama da fararen hula 100,000.
Addinina da hankalina da kuma ganin yakamata sunsa dole nayi Allah wadai da wannan mummunar akida da kuma kasarda ke aikata hakan. Babu kuma wani dalilinda zaisa na aminta da wani huhulahu na cewa wai wannan azzalumar kasar nada yancin kare kanta ko yancin zama kasa koma yancin wanzuwa.
Babu wata kasa musamman kasarda aka kirkira bisa zalunci, cin amana, zubarda jini tare da handama da babakera da keda yancin zama kasa ko ci gaba da wanzuwa.
Azzalumi bashida wani yanci na cigaba da zalunci, kisan kiyashi, kisan gilla, handama da babakere.
Mahandami, azzalumi, mai yiwa mata da kananan yara fyade, barawon filayen jama,a, mai tabargaza da barazana ga rayuwar mata da kananan yara bashida wani yancin wanzuwa saidai damarda ya bawa kanshi bisa zalunci, handama da babakere.
Yana wanzuwa ne, yana kuma aikata barna da fasadi a bayan kasa bawai don yanada yancin yin hakan ba sadai domin yanada karfin yin hakan ba tare da wani hukunci ya shafe shi ba.
Abun lura da la,akari ne cewa anyi manyan kasashe da dauloli masu karfin mulki a baya amma kuma manyan kasashe da dauloli masu karfin fada aji sun shude a baya. Komai mai shudewa ne.
Wannan itace al,adar duniya, babu wani abu mai dawwama a cikinta saidai ikon Allah, haka tarihi ya nuna.
Daulolin Babila, Habasha, Ruma, Ingila, Rasha, Girka, Masar sunyi zama kololuwar karfi da mulki, amma a yau suna ina?
Sunyi lokutansu, wasu sun shafe daruruwan shekaru suna mulki, cika da karfin soja, ilimin zamaninsu dama arziki da daudar duniya, amma daga karshe sun bata a ribibi sun zama tarihi kamar ba,ayi ba. Sun komai kufai abun kwatance.
A cikin wannan rintsin, yancin wanzuwa, yancin kare kansu dama duk wata dama da suke tinkaho da ita ta bace taredasu a cikin duhun dare tare da su, da duk wani abunda suka mallaka.
Wannan shine sakamakonda ke jiran kasar Zayonawan Israila idan har basu tuba ba suka koma ga Allah.
Misalinta daidai yake da misalin gagarumin sarkin Rumawa Julius Caesar tazo, ta gani ta kuma mamaye.
Daga lokacinda aka sake kafa kasar ta Israila shekaru 75 da suka gabata batada aiki sai tinkaho, alfahari da kuma nuna isa da karfin mulki. Alfahari da nuna dukiya da ilimin kimiya da fasaha da kuma karfin mulki musamman akan Falasdinawa farar hula.
Duba da kalaman budurwar Babila wacce littafin Ishaya a cikin Attaura yayi bayani da take cewa ” nice, kuma babu wata baya na!”
Amma dukda cikarta da batsewa da kuma makancewarta ta hanyar alfahari da nuna isa da tumbatsa da kuma yin kunnen uwar shegu da duk wata shawara ko wa,azi akan irin ta,addancinda kasar ta Israila ke aikatawa a zirin Gaza. Dubunta ya cika tabbas Allah ubangiji zai kamata, kamu mai tsanani kamar yadda ya aikata shekaru 2000 da suka shude kafin a giciye Yesu almasihu.
Tabbas Allah zai karya kashin bayanta, ya ruguza yancin wanzuwarta, ya wofantarda duk wani karfinta tare da hargitsa tunaninta, sannan ya rusa duk wata niyyarda takeda ta kafa gagarumar kasar Israila data kama daga lardin misira zuwa iyakacin kasar Iran. Iska yayi kaca kaca da duk wani burbushinta.
Kasar ta Zayonawan Israila batada wani buri daya wuce su tarwatsa su kuma ruguza yancin Falasdinawa na wanzuwa, su share tarihinsu, su kwace kasarsu su kuma goge tunaninsu a zukatan mutanen duniya.
Abun bakin ciki burinsu shine su tabbatarda hakan tare da cikakken goyon bayan shugaban kasar Amurka Joe Biden. Wanda ya nunawa duniya irin makauniyar soyyayarda yakewa kasar Israila. Haka kuma yayi kunnen uwar shegu da kiraye kirayen kasashen duniya tare da ci gaba da bada goyon baya ta hanyar bada makamai, taimakon sojoji, kudi da sauran kayan yaki tare kuma da taimakon diflomasiyya ga kasar ta Israila, wanda hakan ne ke bawa kasar damar ci gaba da kisan kiyashi a Faladinu da kuma kudurin shafe Falasdinawan daga bayan kasa.
Mu danyi la,akari da wannan.
Duk wani karfi na mulki kona soja ko goyon bayanda take ganin tanada bazata taba cimma wannan burin ko kudurin ba.
Abu mafi muhimmaci shine sannu a hankali dubunta zai cika kuma lokaci zaizo da za,a shafe kasar ta Israila daga bayan kasa.
Saboda Allah ba azzalumin bawa bane kuma shine mai cikakken iko a lamurran mutane.
Littafi mai tsarki ya fada mana cewa buwayi gagara misali bayada saurin fushi kuma ba mai iya cinshi da yaki, mai karfi ne, isashshe, buwayi kuma gagara misali, mai tsananin kamu ga azzalumai.
Shine mai karfin yaki, shin akwai mai iya ja dashi? Kamar yadda Littafi mai tsarki ya tambaya?
Shine gatanmu maganin wudanda suka damemu, kuma baya barin zaluncin azzalumi ya dore kan wanda ake zalunta.
Shine mai cire manyan sarakuna daga kujerunsu, shine mai daukaka kaskantacce ya azirta talaka ya kuma daga wanda ba kowa ba.
Shine uba ga masar uba kuma miji ga bazawara.
Shine gatan talaka, mai taimakon maras galihu mai kuma ramawa wanda bazai iya ramawa kanshi ba.
Shine wanda ya kira kanshi da ” Nine ni, dadadde, na farkon farko, sarkin sarakuna, buwayi gagara misali, maiyi koda kuwa kowa bayaso. Wanda ya haramtawa kanshi zalunci yake kuma taimakon maras galihu shine Allah.
A takaice dai babu wata kafa ko madafa a wannan duniya ga azzalumi mai wariyar launin fata, kisan kare dangi, babu wani yanci ga kasar zayonawa masu irin wannan burin.
Tabbas kuma babu wani yancin wanzuwa ga azzalumar kasar Israila ko azzaluman shuwagabanninta , tabbas tunaninsu da ayukansu basu nuna mutanenda suka dace da wanzuwa ba.
Sun wofantarda wannan yancin daidai lokacinda sukasa kafa sukayi falaci da dokar kasa da kasa ta hanyar kisan mata da kananan yaran Falasdinawa a matsayin abun nishadi da wasanni.
Haka kuma yan anshin shatansu da abokananda suka zagayesu basu taimakawa al,amarin ba.
A misali sunyi nutso a cikin haukansu tare da amfani da yan wasan kwaikwayo irinsu sabon shugaban kasar Ajentina a lokacinda daya kai ziyara kasar Israila kwanakinda suka gabata, bayan yayi addua a bangon kuka, yake kuma yi kira ga kasar Israila data rushe masallacin kudus ta kuma gina sabon majami,ar Yahudu a gurbinsa. Yayi hakane ba tare da la,akari da irin harzuka al,ummar musulmin duniya da wannan matakin zai kawo ba. Tabbas wannan zai janyo yakin duniya na uku, zai kuma iya kawo karshen kasar ta Israila.
Tabbas barewa bata gudu danta yayi rarrafe, shin me kuke tsammani daga shugaban kasarda ta taba yiwa bakaken fata yan asalin kasar ta Ajentina kisan kare dangi? Kasarda aka gina akan zalunci, cin amana da wariyar launin fata, da ta kasance aljannar sojojin Hitla na Nazi a lokacin yakin duniya na biyu?
Tabbas kusanci ga abokai irinsu Javier Milei na Ajentina yasa yahudawa basuda wata bukatar makiya.
Ko shakka babu wannan ba itace irin kasar Israilan Annabi Dawuda bace, babban sarkin da ya taba mulkin Israila ba, wanda akayi ittifaki da cewa shi din badadin Allah ne.
Wannan ba itace Israilan Firam minsita Golda Meir bace, wadda ta taba ikirarin cewa ita Bafalasdinuwa ce.
Wannan ba ita bace kasar Israilan da Firam Minista Yitzhak Rabin bace wanda yayi gwagwarmayar kawo zaman lafiya da Larabawa wanda hakan yayi sanadiyyar yan uwanshi suka kasheshi.
Wannan itace Israilan Bibi Natanyahu, mai kishin jini, dan ta,adda wanda a tarihi ma ba cikakken Bayahude bane, shugaban azzaluman Zayonawa makiya zaman lafiya.
Israilan shi ba itace Israilan da can baya ba, ba itace Israilan da littafi mai tsarki yayi bayani akanta ba, ba itace Israila mai tsoron Allah ba. Wannan itace Israilan iyalan gidan Rothschild, Israilan zayonawa, Israilan Shedan.
Israilan shi ba itace Israilan kasarda Allah ya albarkata ba, amma itace Israilan da ta manta da Allah, ta manta da dokokin Allah, Israilan rashin imani da tausayi ba jinkai.
Israilan shi ba itace Israilan da malaika Mikail ke tsaro ba kakkautawa ba, saidai itace Israilan da Beelzbub, Asmodeus da sauran shedanun aljannu ke mulki masu kira da alfasha da mugun aiki.
Amma dukda irin wannan rashin imanin da rashin kirkin da Netanyahu ke nunawa kadanne idan aka hadashi da irin rashin mutumcin da azzaluman mukarrabansa da ministocinsa ke nunawa. Ministan tsaron sa Itamar Ben-Gvir wanda yake cewa ya kamata a kora Falasdinawa zuwa Saharan Sinai ko kuma a watsasu cikin teku. Wane irin tunani ne na cewa a kora mutane milyan biyu da rabi a warwatsa su zuwa kasashe dari ta hanyar tura mutane 25,000 zuwa kowace kasa. Haka kuma ministan al,ada Ben Eliyahi yake cewa wai ya kamata a harba bomb din nuliya zuwa zirin Gaza. Wato a kashe duk mata da kananan yaran dake zirin Gaza.
Idan har kana mamakin irin wannan rashin tunani da rashin imani to kadan kaji, bari in gutsuro maka wata baranbaramar daga cikin ministocin Netanyahu kamar su Gila Gamliel da kuma ministan kudi Bezalel Smotrich.
Tasu irin tsana da kuma kin jini ya wuce duk inda ake tsammani.
Shin akwai wani dake tunanin cewa irin wudannan azzaluman macuta sune zababbin Allah?
Mai yiyuwa an zabesu amma da ganin irin halinsu da kuma irin ayukansu to babu shakka Shedan ne ya zabesu ba Allah ba.
Tunanin ayi amfani da bomb din nukiliya a sheke mutane sama da milyan 2.5 tunanine na zalunci, tunani ne na shedanci mai kama da irin tinanin Sojojin Hitla na Nazi.
Wannan tunani bashida wajen zama a duniyarmu ta yau koda Bayahude ne ko ma wane irin yare keda irin wannan mummunan tunanin.
Kasar Israila danasani, danake yiwa addua kullum, wacce aka fada a littafi mai tsarki, ba daya take da kasar Israila ta yau ba da aka gina akan turbar wariyar launin fata, kisan gilla, kisan kiyashi da kuma kishin zubarda jini ba. Wannan wata daula ce a karkashin mulkin Bibi Netanyahu dake yaudaran kanta da cewa wai itace kasar Israila wacce keci dasha da jinin Falasdinawa, mata da kananan yara.
Kasar Israilan da na sani, kasace mai cike da so da kauna da yalwata da kuma jinkai da zaman lafiya. Amma Israilan Netanyahu tsinuwa ce ga duniya kuma tawayace da kuma duhu ga duniya.
Ga duk wasu masu ikirarin soyayya ga kasar Israila wudanda ke ganin sunfi karfin doka, kuma zasu iya aikata komai ba tare da gudun hukunci ba. Ina baku shawara daku binciki zuciyoyinku, ku tuna da Allah Ku kuma ji tsoron gobenku.
Allah bazai taba taimakon kasarda ke ganin tafi karfin doka ba. Ku binciki zuciyarku, ku kuma sani cewa Allah ba azzalumin bawa bane.
Allah bazai taba goyon bayan irin zalunci da rashin imanin da Israila keyi a zirin Gaza ba.
Ku sani ku tabbatarda cewa duk wani zalunci yana da adadi.
Su kuma Falasdinawa dake cikin halin kakanikayi da kuma masu tayasu yakar zalunci da handama da babakere ku sani cewa tabbas dare nada duhu da ban tsoro amma duk bayan tsanani sauki na nan tafe.
Kuyi man uzuri in kare wannan sashen da tarihi da kuma gwagwarmayar wudannan Falasdinawan da Israila ke burin ta kwace kasarsu ta kuma share tarihinsu.
Tunda Falasdinawa suka zabi jam,iyyar Hamas a zaben shekarar 2006 kasar Israila ta mayarda zirin Gaza zuwa sansanin yan gudun hijira, wata budaddiyar gidan yari.
Tun daga lokacin duk wasu kayan masarufi dake shiga zirin Gaza bazai shiga ba saida izinin kasar Israila.
An zagaye zirin na Gaza, ba wani ko wata da zai ko zata shiga zirin saida izinin Israila
Dadi da kari babu wata kasa ko kungiya a fadin duniya da aka yarda su taimaka masu ta ko wacce hanyar ba tare da izinin kasar Israila ba. Babu wani abunda zai iya shiga zirin Gaza saida izinin Israila.
An mayarda su kamar wasu kebabbun beraye, a wani sansanin soja, an zagayesu ta kasa, ta ruwa da sama. Baya da haka babu masaka tsinke a Gaza da ruwan bama bamai bai aukawa ba, mata da kananan yara, farar hula da dattijai. Kisan kare dangi da gilla daga sojojin Israila da shinge daga sojojin Israila, sohojinda basu taba cin nasara akan wasu kwakkwaran sojojin ba saidai kisan kiyashi akan fafaren hulan Falasdinawa hadi da mata da kananan yara.
Mazauna kasar Falasdin na zaune cikin kunci, bautarwa da kuma mummunan rashin imani, mulkin mallaka daga sojojin Israila, duk da haka sun jure,sun jajirce ba tsoro ba gudu ba ja da baya.
Abun takaicinda ya kara radadin mulkin mallaka da kisan kare dangin da ake masu da kuma labaran kanzon kurege da jaridun yammacin duniya ke yadawa shine yunkurin sauya gaskiya, canza tarihi, da kuma boye gaskiya. Tabbas Falasdinawa mutane ne masu son zaman lafiya, mutanen kirki masu tarihi daya dauki shekaru aru aru.
Haka kuma Falasdinawa sune mutane mafi ilimi a yankin gabas ta tsakiya koma a duka fadin duniya, kashi 30% dinsu nada digiri na uku wato PhD kuma kashi 99% nasu sun iya karatu.
Akwai Falasdinawa milyan bakwai dake zaune a zirin Gaza, Gabar tekun yamma da kuma kasar Israila, sannan akwai wasu milyan bakwai din dake zaune a kasashe ketare dake ayukka dabban dabban na ilimi da fasaha. Suna kuma karatu a jami,oi dabban dabban a fadin duniya.
Kasashen larabawa na duniya sun juya masu baya sun kuma kasa taimaka masu saboda karfin fada aji na kasashen Amurka da Israila. Amma hakan bai hanasu ci gaba ba a fannin kimiya da fasaha, wasanni dama duk wani bangare na ci gaba a rayuwa.
Sun kasance jajirtattu, wajen bijirewa da kuma bara,a ga mulkin wariyar launin fata, mulkin mallaka da handama da babakeren Zayonawa yan share waje zauna, sun kuma jajirce akan kare hakki, mutunci da kuma muradinsu, koda kuwa hakan zaiyi sanadiyyar rasa rayukansu.
Wannan yunkurin da jajircewa da kuma yunkurin kwatar yanci abun a yaba ne ga mutane masu hankali da sanin ya kamata.
Tabbas wata manuniya ce akan jajircewa, hazaka da kuma juriya kamar yadda marubuci dan kasar Amurka mai suna Franz Fanon ya misalta a littafi shi mai suna “Wretched of the Earth” wato kaskantattun duniya.
Kamar yadda bakaken fata masu rinjaye a kasar Afrika ta kudu lokacin mulkin mallaka na wariyar launin fata a kasar suka mike wajen yakin neman yancin Kansu, dubbansu sukayi shahada a cikin daruruwan shekaru da aka shafe ana masu mulkin mallaka, suka jajirce suka ki bada kai bori ya hau. Kamar yadda dan gwagwarmaya Patrick Henry yayyi kira ga sarki Gorge na uku na kasar Ingila inda yace ka bani yanci na ko ka bani mutuwa, haka suke ihun daga rafi zuwa teku, Falasdin zata samu yanci.
Abun lura ne cewa duk wani dan Gaza da Bafalasdine bashida wani buri da yawuce da ya wuce samun yancin Falasdin zai kuma iya sadaukarda rayuwarsa da dukiyarsa wajen cimma wannan burin, za,a iya ganin hakan idan akayi la,akari da yadda suka jajirce wajen yakar Israila domin neman yanci da kare mutunci.
Suke kera kusan duka makamanda suke amfani dasu, kuma gwarazan mayakansu na amfani da wudannan makaman wajen tarwatsa sojan Israila.
Na kalli ministan harkokin sada zumunta na Gaza Dr. Ghazi Hamad wanda yake daya daga cikin majalisar zartarwa ta kungiyar Hamas a talabijin ranar talata da ta gabata yake hira da Seun Okinbaloye a gidan TV na Channels. Nayi matukar jinjina masa da kuma aminta da hujjojinsa.
Yayi magana mai cike da ilimi da fasaha ya kuma bada hunjoji masu karfin gaske wudanda baza,a iya inkarinsu ba.
Milyoyin yan Najeriya sun sha jinin jikinsu a lokacinda sukaji yadda yake tsage gaskiya dangane da makasudin harin da Hamas ta kaiwa Israila a ranar 7 ga watan Oktoba shekararda ta gabata. Inda yaki ya bada hakuri koya kushe harin. Da kuma yadda ya fede biri har wutsiya akan gwagwarmayarda Falasdinawa suka shafe shekaru 75 sunayi.
Ya bada hujjoji karfafa guda hudu.
Na farko shine duk mutumenda sojojin haure suka mamaye gidanshi, suna kashe mashi mata da yaya kullum ba yadda za,ayi a kirashi da dan ta,adda saboda yayi yunkurin korar bakin haure daga gidan nashi.
A tawa fahimtar wannan hujja ce mai karfi.
Ba yadda za,ayi ka roki mayunwacin dila akan ya bar garken tumaki, ko ka roki mayunwaciyar damisa data bar makwanci kaji, saidai ka koresu da karfin tuwo.
Bakada wani zabi face kayi amfani da makami wajen yakar mulkin zalunci ko kuma ka mika wuya bori ya hau ka mutu a wulakance.
Wudanda suka yarda da karairayin da jaridun yamma ke yadawa akan Hamas tare da kakaba masu lakabin ta,addanci zan yi maku tambayoyi kamar haka.
Tayaya mutumenda ya mamaye kasar mutane yana kwace masu gidaje da karfin bindiga, yana kashesu tare da azabtardasu tayaya zai kira masu garinda yake bautarwa yan ta,adda saboda kawai sunyi kokarin kare kansu da kuma korarsa daga kasarsu dayake kokarin sacewa? Shin wannan shine ta,addanci a idonku?
Tabbas wudannan mutanen baza,a iya jingina masu ta,addanci ba a fuska ta adalci.
Wannan shine misalin abunda ya faru a Afrika ta kudu, bayan daukar shekaru ana mulkin mallaka, wariyar launin fata, handama da babakere daga karshe Afrika ta kudu tayi nasarar kwace kasarta daga hannun masu mulkin mallaka a karkashi jamiyyar ANC. Mai taken kibiyar Afrika ta kudu.
Tarihi na cike da irin wudannan misalan.
Jajirtaccen mai wa,azi kuma bawa daga kasar Amurka Ned Turner yayi irin hakan a jahar Virginia a lokacinda bayi bakaken fata sukayi bore a garin Southampton a shekarar 1831.
Hakama kasar Amurka tayi yakin tawaye akan mulkin mallaka da kama karya inda ta kwaci yancinta a hannun turawan mulkin mallaka na Ingila a shekarar 1775.
Haka Faransa, sunyi bore inda suka fuskanci mulkin kama karya a shekarar 1789 suka kashe sarakunan gargajiyarsu, suka kuma kori mafiyawancin masu rike da madafan iko na gargajiya a wancan lokacin.
Haka Ingila tayi yakin kwatar yancinta a shekarar 1642 a lokacinda Oliver Cromwell ya jagoranci yakin juyin juya hali yakuma samu galabar cireshi daga mulki ya kuma kafa sabon tsarin mulki a Burtaniya.
Haka daular Rasha, suma sunyi bore inda suka yi yakin juyin juya hali a shekarar 1917 lokacinda Vladimir Lenin tare da jam,iyyarsa ta Bolsheviks suka yaki Sarkin lokacin wato Tsar Nicholas na biyu suka cireshi daga mulki suka kuma kafa sabuwar daular USSR.
A kasar Haiti ma Toussant Louverture yayi irin hakan a kasar Haiti a shekarar 1801 a lokacinda ya jagoranci sojojinsa bakaken fata ya fuskanci sojojin mulkin mallaka na Faransa, yakuma cisu da yaki ya kafar kasar bakaken fata ta farko a yammacin turai.
Haka ma anan kusa damu a kasar Ghana Fl. Lt. Jerry Rawlings ya jagoranci mutanen kasar inda suka yaki mulkin kama karya da zalunci a kasar a shekarar 1979 a lokacinda ya gudanarda juyin mulki a kasar sannan kuma ya zartarda hukuncin kisa akan masu rike da madafun iko na wancan lokacin.
Zan iya ci gaba da irin wudannan misalan.
Idan daukar makami a fuskanci mulkin kama karya da zalunci yancin bil Adama ne wudancan kasashen, idan kuma irin wannan yunkurin yayi nasara a wudancan kasashen me zai hana Falasdinawa yin hakan?
Shin su ba mutane bane ko basu kai matsayin sauran mutane bane? Shin ko nauyin mutanensu bai rataya akansu na mikewa su yaki mulkin mallaka ba?
Shin manyan addinan nan guda biyu na musulunci da kiristanci basu bada damar yin hakan ba?
Hujja ta biyu da mai girma minista ya bayar a hirarshi da Channels TV a yayinda ake tambayarsa shin Hamas zasu saki saura kamammun Israilawa sama da 100 dake hannusu itace, tabbas Hamas zata sakesu idan har Israila ta saki Falasdinawa 5000-7000 dake daure a gidajen kason Israila, wudanda mafiyawancinsu mata ne da kananan yara da suka kama a zirin Gaza da kuma yamma da kogin Jordan shekaru da kuma watanninda suka gabata.
Da aka tambayeshi akan kisan mata da kananan yara da Hamas tayi a harinda ta kaiwa Israila a ranar 7 ga watan Oktoba ministan yace Sam ba niyyar Hamas bace kan cewa su kashe mata da kananan yara ya kuma tabbatarda cewa Israila ta dauki watanni da kuma shekaru tana kashe mata da kananan yara a Falasdin amma duniya tayi zuru tana kallonsu ba tareda cewa uffan ba.
Duk da cewa a fahimta ta kuskure biyu bazasu zamo daidai ba amma wannan hujjar tashi abar dubawa ce.
Shin mata da kananan yaran Falasdinawa ba mutane bane ? Shin ba jini da jijiya bace a jikinsu? Shin basuda yancin su rayu?
Israila ta shafe shekaru tana aikata kisan killa a Falasdin haka kuma wannan kisan kiyashin ya dauki sabon salo tun bayan harinda Hamas ta kai Israila a ranar 7 ga watan Oktoba. Kisan mata da kananan yara ya bude wata sabuwar kafa da rashin imani, zalunci da mugunta a duniyarmu ta yau.
Mutanenda koda mutuwa wani daga cikin fursunonin Falasdin sukayi a gidajen kason Israila, sojojin basa bada gawarwakin mamatan ga yan uwansu domin ayi sutura a binnesu bisa al,adar Falasdin.
Zayonawa sun kashe sama da mata da kananan yara 17000 a Falasdin sun raunata dubbai a watanni hudu da suka shude kuma duk da haka suna ikirarin cewa sune keda damar kare kansu?
Wannan ba hujja bace da zata taka kara ta karya ba, duk da munin al,amarinda ya faru a ranar 7 ga Oktoba ramuwar gayya data biyo daga Israila abun ayi Allah wadai ne, aikin zalunci ne, mai kama da kisan kiyanshinda Nazi suka gudanar a yakin duniya na biyu.
Abunda Hitla da Jamusawa suka yiwa Yahudawa a shekarun 1936-1945 shine kalar abunda Zayonawa keyiwa Falasdinawa a yau.
Jamusawa sun kira hakan a wancan lokacin da sunan mafita ta karshe ayau na kira wannan aika aikan da sunan mafita ta karshe.
Banbancin kawai shine launin fatar wudanda ake bautarwa ya canza kuma wanda ake farauta yanzu shike farauta.
Daga karshe yayi manuniya da cewa dukda yake duniya tayi biris da mawuyacin halinda Falasdinawa ke ciki, haka kuma hanyar diflomasiyya da gwamnatin Falasdin ta dauka karkashi jagorancin Mahmud Abbas bai cimma wata muhimmiyar nasara ba kawo yanzu shekaru 30 kenan. Yayi ikirarin cewa koda kowa ya juyawa Falasdinawa baya to Hamas bazata taba juyawa musu baya ba, ba kuma zasu daina gwagwarmaya da makami ba domin kwatar yancin su ba.
Shin akwai wani wanda zai soki wannan lamirin? Nidai bazan iya ba.
Musamman ma idan aka yi la,akari da fadar Natenyahu akan cewa bazai taba yarda da akafa kasar Falasdin ba. Da kuma duba da cewa yayi facakali da yarjejeniyar Oslo da Amurka ta jagoranta.
A tashi fahimtar, shi da masu irin tunaninsa iya abunda ya dace da Falasdinawa shine kawai a sheke su, a kawarda su daga doron kasa ko kuma a ci gaba da gallaza masu da bautardasu da ci gaba da masu mulkin mallaka.
Duba da irin wannan shin akwai wani dalili dazai hana duk wani mai ilimi da hankali bazai mike ba ya dauki makami domin kwatar yancin sa?
Shin baifi dacewa ba da mutum ya mutu rike da makami ba daya kwanta azo har gida a sheke shi?
Wannan shine tunanin Hamas kuma abun dubawa ne da kuma lura ga mai hankali.
Ba abun mamaki bane da dan siyasar nan na Afrika ta kudu Julius Malena yace duk wani wanda bai goyi bayan Hamas ba a gwagwarmayarda suke shashasha ne.
Na yaba da kokarin Seun Okinbaloye daya bayarda dama ga Mr. Hamad domin ya fito duniya ya bada fede gaskiya akan gwagwarmayar suka share shekaru akai.
Jakadan Israila mai suna Michael Freeman wanda shima ya hallaci wannan shirin na Channels TV kashe gari yayi yunkurin kwashe tabarmar kunya, ya kasa samun natsuwa da kamala, bai fadi wani abun azo a gani ba face zuke ta malle.
Babu abunda yayi face karairayi da kuma shirmen kwasar karan mahaukaciya. Kuma yayi hakan cikin alfahari da girman kai da dagawa a gaban duniya.
Ya kasa kafa wata hujja kwakkwara da zata gamsarda mutane dangane da karairayinda yake fesowa. Baiyi komai ba sai maimaita tatsuniyoyinda yahudu suka dade suna yaudarar duniya dasu.
Ina ganin kahonnin shedan guda biyu yadda suke lekowa a kansa da warin wutar jahannama yayinda yake feso karairayi, yaudara, yada gulma da munafunci, tsatsangaryar kiyayyar larabawa da ta,addanci irin na yahudawa zayonawa.
Ina zargin babu wani wakilin shedan a bayan kasa, mai guba a harshe, makaryaci, azzalumi, mayaudari, makashin mata da kananan yaranda basu ji basu gani ba kamar sa.
Koda Freeman yanaso ko bayaso jawaban Mr. Hamdan a Channels TV sun bankado tare da tona karairayin da kasar Israila ta shafe shekaru tana yadawa, sun kuma bude idona dama milyoyin yan Najeriya akan irin halin Israila na handama da babakere, kisan kiyashi, mulkin mallaka ya kuma kore karairayi da ake yadawa akan cewa Hamas yan ta,adda ne kuma wudanda basa kula da hakin dan Adam.
Tabbas su ba wasu maridan dodanni bane, masu kishin zubarda jini ba, ba kuma jahilan azzaluman yan ta,adda bane masu muradin fasadi da barna a bayan kasa kamar yadda jaridun yammacin duniya ke yadawa. Sabanin haka ya nuna cewa mutane ne masu sanin ya kamata, masu kishin al,ummarsu masu kuma zimmar kare kasarsu da mutuncin jama,arsu.
Babu mamaki da har wayau Zayonawan Israila suka kasa cinsu da yaki, suka kasa ganin bayansu duk da cewa akalla kashi 70% cikin 100% na Falasdinawa an taba ko an sha dauresu a gidanjen kaso na Israila.
Ba kuma abun mamaki bane da cewa idan za,a sake zabe yau a zirin Gaza to Hamas zatayi nasara kamar yadda tayi a zabenda ya gabata.
Wannan itace gaskiya mai dacinda duniyarmu ta yau batason ji.
Muna rokon samun zaman lafiya mai dorewa muna kuma rokon Allah ubangiji muna zubarda hawayenmu ya ubangijin Ibrahima, Ishaka, da Yakuba, Ubangijin Israila ka kawowa Falasdinawa ɗauki ka kuma yi masu sakayya.
Cif Femi Fani Kayode, Tsohon ministan Sufurin Jiragen Sama na Najeriya
Discussion about this post