Duk da famar da ‘Yan Nijeriya suke ciki ta matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa, musamman ga ma’aikata, zai yi mutakar wahala Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta iya samar da sabon tsarin albashin da zai zama gamsasshe ga ma’aikata.
Duk mai nazari zai iya fahimtar cewa, wannan tsananin talauchin ba kawai al’umar Nijeriya yake addaba ba hatta ita kanta wannan gwamnatin ta Shugaba Tinubu na fama da karanchin kudi, duk da kasancewar ta janye tallafin man fetur kuma ta karya darajar kudin kasar a fakaice.
Dalilan da yasa zai wuya ita wannan gwamnatin a wannan yanayin ta iya yin sabon albashi sun hada da:
Kasa Biyan Basukan da Ma’aikatan ta suke binta.
Da yawa da ga cikin Ma’aikatan wasu hukumomi karkashin gwamnatin Tarayya suna bin basuka, wasu na albashin su, wasu kuma na Karin girma, wasu ma sabbin ma’aikata ne, duk da ana sanya wannan kudade a cikin kasafin kudi, amma gwamnatin ta kasa biyan wannan ba suka, saboda karanchin kudin da gwamnatin ke fama da ita.
A yanzu fa Ma’aikatan dukkanin manyan makarantun Nijeriya da suka hada da Jami’oi gwamnatin ta gaza biyan su Karin albashin da a ka yi musu tun lokacin gwamnatin Buhari, duk da kasancewar wannan gwamnatin ta bada umarnin a sanya musu sabon karin albashi na kashi 25 da kashi 35, tun a watan Satunbar 2023.
Bayan wannan, in za mu iya tunawa, yajin aikin karshe da Ma’aikatan Jami’oi har da ASUU suka yi, wanda ya jawo rike musu albashin su har na tsawan watannin takwas da kuma afuwar da Shugaba Tinubu yayi wa Ma’aikatan na yarjewa biyan su albashin watanni hudu daga ciki, yanzu kimanin watanni biyar kenan wannan alkawarin ya gaza cika.
Ko a yanzun ma a kwai barazanar komawar Malaman Jami’oi wato ASUU komawar su yajin aiki, bisa dalilan kin cika alkawarin da suka yi da gwamnatin.
Shi Kansa alkawarin da gwamnatin tayi da kungiyoyin kwadago na bada tallafin dubu 35 ga dukkanin ma’aikaci, yana neman ya ci tira.
Shi kansa bada tallafin dubu 25 ga marasa galihu, shima ya tsaya, duk da kasancewar, yin kwaryakwaryar kasafin kudin da gwamnatin tayi a bara.
Su kansu kungiyoyin kwadago sun bawa gwamnatin wa’adin mako biyu a kan wannan alkawarin nasu ko su suma su dunguma yajin aiki.
Duk fa wannan gazawa ta Gwamnatin Tarayya ya ta’allaka ne da karanchin kudin shigowar da gwamnatin ke fama da shine.
Ba a ma maganar gwamnatocin jahohi wanda basa iya ma biyan karin albashin da a kayi na shekara biyar da suka wuce na dubu 30, wasu ma a cikin su basa iya bada tallafin rage radadin cire tallafin man fetur ba.
A kwai Jan aiki kwarai a gaban gwamnatin da ma kungiyoyin kwadago wajen aiwatar da sabon albashi a wannan Lokacin.
Discussion about this post