Bayanan da kasuwar hada-hadar musayar kuɗaɗe ta buga sun nuna cewa Naira ta yi tsallen-baɗake ta kai Dala 1 kan Naira 1,5550, sai kuma daga baya ta tsaya a Naira 1,534.39 a ranar Litinin.
Sai dai kuma a ranar Juma’a an sayar da Dala Naira 1,489.
Wannan lamari ya faru daidai lokacin da ake fama da raɗaɗin tsadar rayuwa da kuma zanga-zangar neman mafita.
A ranar Talata ɗin nan zanga-zanga ta ɓarke a Sakkwato, bayan cikin makon da ya gabata an yi zanga-zanga a Minna, babban birnin jihar Neja.
Ana cikin wannan hali kuma, sai Bankin Dada Lamuni na Duniya (IMF), ya shawarci Najeriya ta ƙara rufe ido ta cire ɗan sauran tallafin fetur da tallafin kuɗin wutar lantarki, domin ta magance matsalolin da suka dabaibaye tattalin arzikin ƙasa.
IMF ta ce kuɗaɗen tallafin su ne ke ƙara damalmala tattalin arzikin Najeriya.
Bankin ya ce kuma wannan matsala ta tallafi ce ke ƙara rura wutar talauci da matsalar abinci.
A cikin rahoton da IMF ya fitar kan Najeriya, IMF ya bayyana muhimmancin cire tallafin fetur da na wutar lantarki domin a karkatar da maƙudan kuɗaɗen tallafin da gwamnati ke ɗaukar nauyin biya wajen yin ayyukan raya ƙasa da raya al’umma da kuɗaɗen.
IMF ya bayar da wannan shawara ce a halin yanzu da ake tsakiyar fama da raɗaɗin tsadar rayuwa da masifar tsadar kayan abinci, wadda ba a taɓa fuskantar irin ta ba a tarihin Najeriya.
Amma kuma IMF ya bada shawarar cewa gwamnati ta ɗan yi wa marasa galihu wani ɗan ihisanin rage masu raɗaɗin tsadar rayuwa.
“Tallafin fetur da tallafin kuɗaɗen wutar lantarki waɗanda gwamnati ke biya, talakawan da ake yi don su ba su samun alfanun abin. Don haka a cire tallafin kwata-kwata. Amma gwamnati ta yi wa marasa galihu ɗan ihisanin rage masu raɗaɗin tsadar rayuwa, bisa la’akari da halin tsadar kayan masarufin da ake fama da shi.” Inji IMF.
Najeriya ta cire tallafin man fetur a ranar 29 ga Mayu, 2023 da nufin bunƙasa tattalin arzikin ƙasa da kuɗaɗen. Lamarin dai ya haddasa mummunar tsadar rayuwa da tsadar kayan abinci wanda ba a taɓa fuskanta ba.
Wannan masifa ta kai ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu bayyana wasu shirye-shiryen rage raɗaɗin tsadar rayuwa, amma har yanzu shiru talaka bai ga komai a ƙasa ba.
Yayin da gwamnatin tarayya ke ƙara samun kuɗaɗen shiga a kullum fiye da lokacin gwamnatin Buhari, an rasa abin da ake yi da kuɗaɗenz ganin yadda a kullum kuma gwamnatin da ‘yan Najeriya sai ƙasa nausawa cikin masifar durƙushewar tattalin arzikin ƙasa da tsadar rayuwa ake yi.
Gwamnatin Tarayya ta kasa biyan albashin ma’aikata na watan Janairu kan lokaci, har sai da ta kai wasu yawancin ma’aikatun ma sai a ranar 8 ga Fabrairu ko 9 ga wata suka ji ‘alat’.
Discussion about this post